Tarihin Mace A Al'adu



Haka nan game da mata da yara duk da sun hukunta cewa ba a kashe su in an kama gari da yaki, amma sai suka jingina wa Musa (A.S) karyar cewa ya kashe mata da dukkan yara da duk wata mata da namiji ya taba kusantar ta a lokacin da ya ci nasara a kan wani gari domin su cimma burinsu irin wannan a kan mace. Game da gado kuwa matukar uba yana da da namiji to mace ba ta da komai, amma duk da irin wadannan dokokin ba mu ganin ana sukan wannan addini a matsayin wani Addini da ya tauye hakkin mace. Hada da cewa a bisa dokarsu adadin matan da za a iya aura ba kayyadadde ba ne, amma ba mu ga mai suka ba a kan hakan kamar yadda ake sukan musulunci[20].

A kissoshin Annabawa da suke cikin Attaurar ya zo game Annabi Sulaiman (A.S) yana da mata dari bakwai da kuyangi dari uku, Dawud (A.S) yana da mata biyu, haka ma Ibrahim (A.S). Kuma matar Musa (A.S) Maryam ta yi wa Haruna (A.S) magana don Annabi Musa (A.S) ya yi mata kishiya bakar fata ‘yar Habasha kamar yadda ya zo a Littattafansu[21].

A nan ya kamata mutane su yi hukunci tsakanin irin wadannan dokoki da na musulunci, su kuma kwatanta su su ga ni’imar da Allah ya tanada a cikin addininsa na musulunci da kuma kamalarsa, da kula da hakkin mata da maza da ba a taba samunsa ba a cikin wani Addini a tarihin rayuwar dan Adam[22].

Mace A Cikin Kiristanci

Babu wani bambanci sosai a mafi yawan dokoki tsakanin Kiristanci da Yahudanci, misali game da hukuncin lullubi da hijabi wanda akwai shi a Yahudanci da Kiristanci amma sai suka sassauta hukuncinsa, wanda a farkon Kiristanci rashin sanya shi laifi ne kuma aibi ne mai girma da saba doka. Duba ka ga abin da ya zo a Risalar Bulus zuwa ga mutanen Korentis da umarnin a aske gashin duk wata mata da ba ta da hijabi (lullubi) don ta ladabtu[23].

Hakan nan suka sassauta shi saboda faruwar juyin juya halin masana’antu a kasashen turai da sunan saukaka aiki ga mace don ta ji dadin yin aiki a gona da ma’aikatu, sai abin ya yi yawa har coci ta yi muwafaka da shi.

Game da auren mace sama da daya kuwa, wasu sun kayyade shi da hudu, wasu kuma ba iyaka, kamar yadda yake gun Yahudawa, amma sai ga shi an soke musu wannan hukunci duk da kuwa ya saba da kissoshin yawan matan Annabawa (A.S) da suke kawo wa a cikin Injila. Abin takaicin shi ne; ba mu san dalilin sukan auren mace fiye da daya zuwa hudu da wasunsu a yammacin duniya suke jifan musulunci da shi ba alhalin suna da sama da hakan a littattafansu.

Idan ka bincika game da sauran dokoki ka kwatanta su da na Musulunci a nan ne zaka kara godiya ga Allah da ya aiko Manzon Rahama Muhammad dan Abdullah (S.A.W) da wannan ni’ima ta Addinin Musulunci mai tsarin da yake kunshe da warwara ga dukkan matsala ta rayuwa ga dan Adam a Duniya da Lahira.

Mace A Yammacin Duniya

Amma mace a yammacin duniya muna iya cewa: Yammacin duniya sun kwaikwayi musulunci ne amma sai suka dauki wanda ya yi musu da zai taimaka musu a duniyance suka cakuda shi da al’adunsu, wato sun dauki samfur ne, amma suka ki yin aiki da duk abin da ya kunsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next