Tarihin Mace A Al'adu



A yankin Larabawa mace wata kalma ce ta wula- kanci a gaya wa namiji ita, kuma kalma ce ta kaskanci, haka nan mace a wasu al’ummu ta zama murhu ne kawai na dafa abinci ko wanke kaya da yara, sai kuma idan bukatar namiji ta taso, amma duk abin da ya shafi ci gaban al’umma wannan wani abin mamaki ne a ga mace a ciki.

Duba ka ga wurare kamar kasashanmu kusan ala’amarin mace yana da ban takaici ta yadda a komai kana iya ganinta idan ya shafi gida kawai, amma wani abu ko da kuwa na Addini ne da ya shafi al’umma gaba daya ne to a nan wani abin mamaki ne a ganta a ciki, ba ta isa ta ziyarci makabarta ko masallaci ba, ba a ma tunanin wurin mata. Haka ma shugabantar wata kungiya ko kafa wani abu na shugabantar wasu jama’a, sabanin wasu kasashe kamar Farisa da aka samu ci gaba ta wannan bangare da mace tana iya yin ilimi mai zurfi har ta kai matsayin mai iya yin ijtihadi a hukunce-hukuncen Addini, a yau a cibiyoyin ilimi mata sun riga sun mamaye ko’ina har sun wuce maza a fagage da dama.

Mace A Gun Yunan (Girika)[17]

Amma a Yunan[18] al’amarin mata ba shi da bambanci da na Rumawa suna la’akari da namiji ne a dokokin zamantakewa, komai na namiji ne ba abin da mace take da shi, amma a bangaren laifi ana hukunta ta, haka ma in ta jawo wani abu na amfani to wannan na namiji ne, suna ganin mace kamar kwayoyin cuta ne masu cutar da al’umma, amma ta wani bangare abu ce ta amfanin al’umma, kuma idan ta sake ta yi laifi ko yaya yake, to ta shiga uku.

Suna ganin mace kamar wani ribataccen yaki ne da yake kurkuku wanda idan ta kyautata amfani ba nata ba ne, idan kuwa ta munana ta dandani kudarta, kuma ba a gode mata, suna ganin tunaninta sharrin ne kawai, saboda haka ba ta isa a bar ta a kan tunaninta ba.

Haka nan maza su ne kawai al’umma, shi ya sa gidan da babu maza hukuncinsa a rusa shi, don haka idan wani ya ga ba ya haihuwa to dole ya ba da aron matarsa don a yi mata ciki a samu namiji, in ba a samu namiji ba sai ya yi tabanni da dan wani ko dan zina ko da kuwa ta hanyar runton da ne da jayayya. Saki da aure a wajensu iri daya ne da na Rumawa, kuma ka kan iya auren mata ko nawa ka so amma daya daga ciki ita ce bisa doka, sauran kuma ba a bisa doka suke ba[19].

Mace A Gun Yahudawa

Yahudawa suna da dokoki wadanda ba su dace da kima da matsayin mace ba, da kuma danne hakkin nufi na dan Adam. A dokokinsu idan da namiji zai auri yarinya, sai ya yi da’awar ya same ta ba budurwa ba, to babanta yana iya kai jini a kyalle kutu ya ce: An yi wa ‘yarsa kazafi, idan ya ci galaba sai a ci mijin tarar azurfa dari, kuma bai isa ya sake ta ba har abada, amma idan aka tabbatar da haka, to ita kam za a kai ta bayan gari ne a jefeta har mutuwa. Duba ka ga ni babu shaida, babu ikirari daga gareta, amma ana iya kashe ta. Wata tambayar ita ce, yaya aka yi uban ya samo jinin budurcinta? Daga ina kuma za a iya tabbatar da haka ko na rago ne!

Haka nan suka ce: Idan mutum ya saki matarsa, ta auri wani shi ma ya sake ta, to na farkon ba shi da ikon sake aurenta domin an najasta ta, abin mamakin a nan yaya aka yi aka najasta ta, ta zama najasar da ba zata iya komawa ga na farkon ba! haka nan yaya maganar idda?

A wata dokar suna cewa ne: Idan dan’uwa ya zauna da matarsa da dan’uwansa a gida daya, sai shi mijin ya mutu, to ya zama dole kan dan’uwansa ya aure ta, idan kuwa ya ki, sai ta kama hannunsa ta kai shi gaban dattijan gari ko yanki, ta cire takalminsa, ta kuma tofa masa yawu a fuska, sannan a rika kiransa da sunan: mai tubabben takalma. Tambaya ita ce: Don me ba za a bari ta zabi abin da take so ba, wa ya sani ko ba ta son sa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next