Tarihin Mace A Al'adu



Idan ka bincika game da sauran dokoki ka kwatanta su da na Musulunci a nan ne zaka kara godiya ga Allah da ya aiko Manzon Rahama Muhammad dan Abdullah (S.A.W) da wannan ni’ima ta Addinin Musulunci mai tsarin da yake kunshe da warwara ga dukkan matsala ta rayuwa ga dan Adam a Duniya da Lahira.

Mace A Yammacin Duniya

Amma mace a yammacin duniya muna iya cewa: Yammacin duniya sun kwaikwayi musulunci ne amma sai suka dauki wanda ya yi musu da zai taimaka musu a duniyance suka cakuda shi da al’adunsu, wato sun dauki samfur ne, amma suka ki yin aiki da duk abin da ya kunsa.

Koda yake a wasu mahangai nasu da yawa sun sha bamban dari bisa dari da musulunci, domin shi ya tsakaita dokokinsa ne a komai, ya kuma dora shi bisa maslaha da hadafin halittar dan Adam ne, amma su sun dauki mutum a matsayin shi ne ma’auni, saboda haka sai ya zama tamkar shi ne Ubangijin kasa wanda komai ya so shi ne daidai, kuma ba a hana shi cimma abin da ya sa gaba. Wannan duk da sunan ‘yanci da hakkin dan Adam, ta wani bangaren kuma suna kokarin nuna wa duniya kamar shi musulunci bai kula da hakkin dan Adam din ba.        

Musulunci yana kunshe da dokoki da babu wani Addini ko ra’ayi da ya kai shi kula da hakkin dan Adam, ya kuma sanya mutum a matsayin bawan Allah, ba bawan mutum ba, ya girmama mutum, ya sallada shi a kan sauran halittu da samammu, amma ya sanya masa sharadi ne na kada ya shiga hakkin wani, kuma kada ya saba wa hakkin Ubangijinsa, domin akwai hakkin Allah da na sauran bayi a kan dan Adam da ya zama dole a kula da shi, kai har ma da hakkin sauran dabbobi da halittu.

Yamma da suke ganin cewa sun daidaita mace da namiji a komai a nazarinsu da mahangarsu amma sai muka ga sabanin haka a aikace, domin har yanzu ba a samu wata mahanga ba mai iya yiwuwa a aikata ta a aikace in banda mahanga ta musulunci, sannan ga su da tsananin take hakkin mata, har ma dankwali da mayafi da zata sanya a kanta da ganin damarta amma hakan yana iya haramta mata shiga ajin karatu da haramta mata yin ilimi har abada.

Abin mamaki yayin da namiji ya kan shake wuyansa da nektayel yana sanye da dogon wandonsa da ya rife shi gaba daya, amma mace idan ta yi hakan ta lullube jikinta gaba daya wannan abin yaka ne a wajansu, kuma yana kai wa ga abin da muka ambata.

Haka nan yake dangane da Dimokradiyya da ake kira na cewa, mutum shi ne yake tafiyar da mulkin kansa, kuma yake zabar abin da ya ga dama, mun ga wannan ma ya kasa aikatuwa a aikace. A bisa misali; da za a yi zabe a kasa sai a cikin mutane miliyan dari miliyan goma sha biyar su shiga zaben a cikin masu zaben, sai miliyan takwas su yi rinjaye a kan miliyan bakwai. Tambaya a nan ita ce; Yaya za a yi da hakkin sauran miliya shas’in da biyu, Yaya hakkin sauran wadanda ba su yarda ma da tsarin ba, Yaya kuma batun hakkin wadancan miliyoyin da ba su yarda ba da nasu kuri’un?

Amma Musulunci Akida ce kuma tsari ne da yake duk wanda yake musulmi to dole ne a bisa abin da yake cewa shi ne; Shi a yau ya yarda da tsarin musulunci a matsayin abin da zai mallaki rayuwarsa a dukkan bangarorinta na daidaiku, da ta al’umma, da ta gidansa, kai har ma da Lahirarsa, domin maganar ba ta tsaya a duniya ba kawai, kuma dukkan wanda yake cikinsa ya yi imani da tsarin da ya kunsa har a zuci.

A yamma da ake karyar an daidaita mace da namiji a hakkin komai ba tare da la’akari da dabi’ar kowanne da Allah ya halicce shi a kan ta ba, sai ga shi a aikace ya nuna karya ne ko kuma ma ba za a iya aikata shi a aikace ba. Misali yau shekara fiye da dari biyu da kafa kasar Amurka amma mutum nawa ne mace ta rike shugaban kasa, ko mataimakinsa, ko shugaban majalisa, ko ministan shari’a, kai koda na harkokin waje nawa ne, da wasu mukamai da dama da ka kan iya kwatantawa? Haka ma a aikin soja mata nawa ne kuma maza nawa ne? Da yawa mun ga mata sun zama kayan talla da kuma abin biyan bukatar sha’awece-sha’awecen maza a irin wadannan kasashe[24].

Ra’ayin turai shi ne; mace ta samu cibaya ne sakamakon mummunar tarbiyyar da a ka yi mata ne a tsawon shekarun duniya, da kuma ganin da ake da shi game da ita, in ba haka ba, dabi’arta daidai take da namiji. Amma mu muna cewa: Ya kamata su kawo dalili a kan abin da suke cewa, ba kawai da’awa ba dalili ba, mu ba mu taba ganin wata al’umma da dabi’ar halittar mazanta da matanta ya zama iri daya da ma’anar da suke fada ba[25].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next