ZamaninBayyana



- Bayyanar masu da’awar annabta (masu da’awa 60)

- Juyin juya halin masu rauni a kan masu girman kai.

- Bayyanar Dujal.

6- Faruwar abubuwa 5 wadanda faruwarsu dole ne a cikin wasu watanni[9]:

- Bayyanar Sufyani.

- Kisfewa da ruftawar kasa.

- Kashe Nafsuz zakiyya.

- Kira daga sama cewa Mahadi (A.S) zai bayyana da kuma neman yi masa bai’a.

- Bayyanar Yamani

7- Shugabancin tattaunawar azzaluman kasashe kafin bayyanar Mahadi (A.S) wanda zai sanya yaduwar zalunci a duniya ta yadda za a kirga samuwar adalci wani abu ne wanda ba zai yiwu ba.

8- Yankewar kauna daga mutane daga samun gyara da kaunar samun wani mutum daga wajen Allah wanda zai zo domin tseratar da mutane, koda yake wannan al’amari yana bukatar gyara daga su kansu mutane domn Allah ba ya canza wa mutane abin da yake garesu har sai sun canza abin da yake ga kawukansu. (Ra’ad: 11)

Faruwar wannan canjin daga kawukan mutane da kuma taimakon Allah shi ne zai iya bayar da damar bayyanar Mahadi (A.S). Don haka ne neman bayyanarsa daga wajen Allah a aikace da mutane zasu yi yana daga cikin abin da zai sanya hakan, ba kawai a lafazin (maganar) baka ba.

9- Faruwar neman tattauna domin samar da adalci a duniya baki daya. Wannan kuwa zai kasance ne alhalin tattaunawa bisa yin zalunci ta riga ta yadu a duniya kuma ta mamaye ta, sai tattaunawa a kan yin adalci ta zo domin maye gurbin hakan wanda yake yana da alaka da bayyanar imam Mahadi (A.S).

10- Samuwar mutane masu tsarkin zuciya da sadaukarwa domin samar da gudanar da adalci, wadanda suka ci jarabawar Allah da daukaka, kuma suna shirye da yaki a cikin rundunar jagoran karshe.

Da izinin Allah bayyanarsa zata kasance, kuma zamanin juyi da cin nasarar adalci zai zo.

 

[1] Tajalli Tauhid Dar Nizame Imamat, Shafi: 44.
[2] Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Sayyid Muhammad Sadar, Shafi: 270 – 271.
[3] Mutawatirai ne ta yadda ya zama mustahili ne su zama karya saboda yakinin da suke bayarwa.
[4] Sayyid Muhammad Sadar Tarih Gaiba Kubura, Shafi: 289 – 347.
[5] Sayyid Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 287 – 296.
[6] Kamil Sulaiman, Ruzegare Rahayi, j 2,Shafi: 701-723. Da Ayatul-Lahi Ludful-Lah Safi Gulfaigani, Muntakhabul Asar, Shafi: 424 – 438.
[7] Littafin da ya gabata, j 2, shafi: 721,hadisi 1721, 1033. Da Muntakhabul Asar, Shafi: 424 – 438.
[8] Littattfan da suka gabata da wasunsu masu yawa.
[9] Abin da ya gabata.

 



back 1 2 3 4 5