ZamaninBayyana



ta yiwu muna iya cewa al’amarin bayyanar imam Mahadi (A.S) a mahangar Shi'a wani abu ne da Allah ya boye shi kuma ya zama sirri domin samun nasarar imam Mahadi (A.S) a kan makiyansa, don haka ne ma ruwayoyi suka zo suna karyata duk wani wanda yake ayyana lokaci; kamar wata ko shekara ko ranar da zai bayyana.

Amma za a iya bayanin alamomin bayyanarsa a dunkule kamar bayyanarsa a ranar ashura ko kwankin da suke wutiri ba shafa’I ba kamar ranar asabar. Sai dai ba yadda za a iya sanin wace ashura ce zai bayyana ko wace asabar ce ko jumma’a. Koda yake ruwayoyin da suka nuna shekarar bayyanarsa a wutiri take ‘yan kadan ne, amma cewa ranar ashura zai bayyana wannan ya zo da ruwayoyi masu yawan gaske da za a iya tabbatar da shi[5].

Ta kowane hali dai ba wanda ya san lokacin bayyanara sai Allah, kuma duk sadda ubangiji ya so ya bayyanar da shi to wannan zai tabbata, sai dai a dunkule idan mun duba ruwayoyi da hadisai zamu ga wannan bayyanar a kusa take idan an samu:

1- Fadawar mutane daidaiku da al’umma gaba daya cikin halin yanke kauna.

2- Gazawar addinan daga samar da abin da suke da’awarsa, kamar tsarin jari-hujja da ya gaza samar da ‘yanci na hakika, da kuma kwaminisanci da ya kasa samar da adalcin zamantakewa da na tattalin arziki da sauransu.

3- Wulakanta kimar addinan Allah a cikin al’ummu kamar bayyanar da munkarai da munanan dabi’u da halaye, kuma da halatta su kamar neman jinsin juna kamar dabbobi, da cin riba, da cin dukiyar mutane, da halatta giya da sauran kayan maye, da yawaitar saki, da karo da juna tsakanin aiki da zance, da cin shubuha, da yawaitar zina da zubar da jini, da halatta yin karya, da cin rashawa, da yanke zumunci, da yaduwar kage da karya, da bidi’o’I, da shugabancin jahilan mutane, da halatta waka da wasanni da muzik.

Da wulakanta mumini, da fakiri, da malami, da girmama fasiki, da azzalumi, da bata hukunce-hukuncen Allah, da halatta dukkan haram din Allah, da take wajiban Allah a kasa[6].

4- Addini da ma’abotansa zasu zamanto baki a cikin al’ummu, kuma kamar yadda mutane a farkon musulunci suka rika shiga cikin addinin jama’a-jama’a (surar Nasr) haka nan zasu rika fita daga cikinsa jama’a-jama’a[7].

5- Faruwar wasu abubuwa na sama da na kasa da suka hada da[8]:

- Yin ruwan sama na kwana arba’in



back 1 2 3 4 5 next