Gaskiyar Addinin musulunci



Na'am yana kan musulmi ya yi bincike bayan tsawon lokaci  tsakaninsa da wanda ya kawo sakon ya kuma san mazhabobin da tafarkuna daban-daban Ya yi bincike Ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar wanda ya kawo sakon Annabi Muhammadu(S.A.W) domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukan hukunce hukuncen da shari'a ta zo da su kamar yadda aka saukar.

Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari'ar da aka saukar kamar yadda take alhali musulmi sun sassaba, jama'a jama'a sun rarraba, babu salla guda, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai ba hatta a bangaren mu'amala... don haka yaya zai yi? da wace irin hanya zai yi salla? da wace irin fuska na daga ra'ayoyi zai yi aikin ibada da mu'amalarsa kamar aure, da saki, da gado da saye da sayarwa da zartar da haddi, da sauransu?

Kuma sam bai halatta gare shi ya bi ra'ay

in iyaye ba ko ya koma ga abinda zuriyarsa da mutanensa ke kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah Ta'ala domin babu wata zazzagawa a nan ba rufa-rufa, babu raragefe babu zurfafawa.

Na'am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da ke kansa tsakaninsa da Allah ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai aibata shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah "Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai." Surar Alkiyama: 36.

"Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne." Surar Kiyama:

"Lalle wannan fadakarwa ce don haka wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa." Surar Muzammil 19.

Tambaya ta farko da za ta fara taso masa ita ce, shin ya kama tafarkin zuriyar gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Bait, zuriyar gidan Manzo (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya "Isna Ashara' masu bin Imamai sha biyu, shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori daban-daban?. ldan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi daga cikin Mazhabobi hudun nan ne ko kuwa daga wasu

Mazhabobi dabam daga cikin wannan bangaren? Haka nandai tambayoyi za su yi ta tasowa ga duk wanda ba ya tunani 'yanci da zabi har ya kai ga gaskiya a bar dogaro.

Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bayani a kan abinda ke biye da ita game da akidar Imamiyya Isna Ashariyya, masu bin Imamai goma sha biyu.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 



back 1 2