Gaskiyar Addinin musulunci



Hanyar tabbatar da gaskiyar Addinin musulunci da sauran shari'u magabata

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin addinin Musulunci za mu iya ja da shi mu tabbatar masa da mu'ujizarsa dauwamammiya wato Alkur'ani mai girma kamar yadda Ya gabata game da kasancewarsa gagarabadau. Kazalika alkur'ani shi ne hanyar sanya mana yakini mu da kanmu yayin da      kokwanto ya fara shigar   mu saboda irin tambayoyin da kan taso wa mutum a zuciya kamar yadda babu makawa kowane mutum mai ‘yanci ya fada cikin irin wadannan tambayoyin yayin karfafa akidarsa da tabbatar da ita.

 Dangane da shari'o'in da suka gabata kuwa kamarsu Yahudanci da Kiristanci ba mu da wata hujja kafin amincewarmu da Alkur'ani kuma idan muka raba kanmu da addinin Musulunci, babu hanyar da zamu gamsar da kanmu ko kuma mu gamsar da mai tambaya, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu'ujiza tasu da ta saura kamar yadda Alkur'ani yake, abinda mabinyan wadannan addinan ke dauke da shi kuma ana zarginsu a kan daukar da suke yi kuma sun sanya hannu a cikinsa. Babu wani abu da ke cikin littafan addinan da suka gabata da ke hannun mutane a wannan zamani wanda ya dace ya zama mu'ujiza madawwamiya mai karfi da za ta yanke hanzari ko dalili mai gamsarwa kafin a yi imani da Musulunci.

Sai daikawai mu musulmi ya inganta ne a gare mu da mu gaskata Annabacin ma"abuta shari'un da suka gabata domin bayan gaskatawarmu da addinin musulunci to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukan abinda ya zo da shi. kuma a cikin abinda ya zo da shi akwai gaskata Annabcin Annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata sashen bayani game da abinda muka yi imani da shi game da Annabawa da littafansu.

Saboda haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari'un da suka gabata, kiristanci da kuma abinda ya gabace shi bayan ya yi imani da Musulunci domin yin imani da shi imani da su ne, imani da shi imani ne da sakonnin da suka gabata da kuma Annabawan da suka shude. Bai wajaba a kan musullmi ya yi bincike game da gaskiyar mu'ujizar Annabawansu, domin abin kaddarawa shi ne cewa shi musulmi ne kuma ya yi Imani da su saboda imaninsa da Musulunci kuma ya wadatar.

Na'am, idan da mutum, zai yi bincike game da addinin Musulanci ya ji cewa bai gamsu ba to lalle ne a kansa kamar yadda hankali da kuma wajabcin neman ilimi suka wajabta Ya yi bincike game da addinin kirista

domin shi ne addinin karshe kafin Musulunci, hazalika idan ya bincika addinin kirista bai gamsu ba to sai kuma ya dukufa a kan addinin da ya gabace shi wato Yahudanci... Haka nan dai zai yi ta bincike har sai ya kai ga yakini yana binciken addinan da suka gabata har Ya tabbatar da ingancinsa Ya yi imani da shi ko kuma rashin ingancinsa ya yi watsi da su baki daya.

Wato sabanin wanda ya tashi a addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da addininsa ba zai wadatar da shi ba ya bar binciken addinin Nasaranci da kuma addinin Musulunci bilhasali ma aiki da hankali da neman sa wajibi ne a kansa kamar yadda hankali ya hukunta, haka nan shi ma addinin Kiristanci bai isar masa ba ya zama ya yi imani da Almasihu (A.S.) wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa. Domin Yahudanci da addinin kirista ba su kore shari'ar da zata zo daga bisani ba wadda za ta shafe ta kazalika Annabi Musa(A.S.) bai ce babu Annabi bayansa ba haka ma Annabi Isa (A.S.) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma yayin da Isa dan Maryama ya ce; Ya Bani Isra'la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abinda ke gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da ke zuwa bayana, sunansa Ahmad. Sai daia lokacin da Ya zo musu da hujjoji bayyanann sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne." Surar Saff: 6.

"Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da addininsu kafin su yi bincike game da shari'ar da ta biyo bayansa wato kamar shari'ar addinin Kirista, da kuma ­addinin yahudanci dangane da Musulunci wajibi ne kamar yadda yake a bisa dabi'ar hankali su yi bincike game da shari'ar da ta zo daga baya.Idan ingancinta Ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta subar  addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace abisa hukuncin hankli su ci gaba da bin addininsu na da tare da riko da shi. Shi kuwa musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da musulunci to ba bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci addininsa da kuma wadanda ake da'awa bayansa. Wadanda suka gabata daia kaddare an san cewa ya yi imani da su don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da ita. Abin kawai da ya hukumta masa game da su shi ne cewa Shari'ar musulunci ta shafe su don haka bai wajaba a aiki da hukunce-hukuncensu kolittafan ba.

Wadanda ake da'awarsu daga baya kuwa dalili shi ne saboda annabin musulunci muhammadu(SAW) ya ce: babu wani annabi bayana". Kuma shi mai gaskisa ne kuma Amini. "Kuma shi ba ya magana a kan son rai ba wani abu ba ne face wahayi da Allah ya yo masa" Surar Najmi: 3-4.

Don haka saboda mene ne ba za a bukaci hujjar da'awar Annabci: da aka yi daga baya ba idan har mai da'awar ya yi da'awa.



1 2 next