MA'ANAR AL'UMMA



wato mutane na nastuwa a cikin shi natsuwa na hutawa. Haka nan Allah Ya fadi cewa:­

"Ka yi salla gare su lalle sallarka natsuwa ce garesu"

wato suna natsuwa da addu'arka, kuma hankalinsu na kwanciya da ita. A wani wuri kuma Ya ce:­

"Shi ne wanda ya saukar da natsuwa a zukatan Muminai"

Ya samar da tabbas da kwanciyar hankali.

Malaman harshen larabci sun yi wadataccen sharhi a

kan kalmar, tare da bayar da misalai, inda duk suka fassara `Natsuwa' da: Kwanciyar hankali, rashin jin kadaici da duk abin da ka sami tabbas tare da zama da shi kuma ka huta da rayuwa tare da shi.2

Da haka za mu iya fahimtar natsuwar da mace ke samarwa ga mijinta da iyalinta, wato shi ne: hutawa, aminci, dauke kadaici, tausayi, albarka da tabbaci, kamar yadda za mu iya fahimtar sirrin zabar wannan kalma mai ma'anoni da yawa, da AIKur'ani ya yi.

Hakika darussa na ilimi sun tabbatar da irin tasiri da yanayin rai da halin mutum ke da shi a kan daukacin harkokinshi cikin rayuwa; saboda a tabbace yake a ilmance cewa ayyukan zamantakewa, alhakin aiki da neman abin duniya, na daga noma, sana'a, hada-hadar siyasa, zamantakewa da hidima ga al'umma kamar ayyukan gudanarwa, aikin injinya, karantarwa, aikin likita, kasuwanci, fannoni da sauran irinsu wadanda kowane daya daga namiji da mace ke yi; duk suna da tasiri kai tsaye daga yanayinsu na halayya. Namijin da ke raye a tsakiyar matsalolin iyali da damuwar zuci da bacin rai, samun shi ga abin duniya kadan ne, haka nan nashadinshi wajen aiki da tunanin kirkiran wani abu cikin ayyukan shi su ma suna tasirantuwa, kuma matsalarsa na karuwa wajen alakarsa tare da abokan aikinsa da wadanda yake da alaka da su.

Da haka dabi'ar alakokin auratayya tsakanin namiji da mace ke taimakawa wajen kyautata matsayin nema da samun, ta hanyar bayyanar tasirinsu na rai da zuciya a kan iyawar mutum da harkokinsa na yau da kullum, da alakarsa da neman abinci da abokan aikinsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 next