MA'ANAR AL'UMMA



Darasi da bin diddigin wadannan ayoyi zai fitar mana da sabubba da dalilan tashin al'umma, wadannan sabubba kuwa su ne:­

1-Tubalin asali na ginin zamantakewa shi ne gamammun dokokin dabi'a na auratayya, wadanda suka hadu daga saduwar jima'i ga mace da namiji; ke nan su ne tubalin asasi na ginin rayayyen zamantakewa ta fuskoki biyu: Abin da zai auku a gaba da halayya.

Wannan alaka wadda ke nufin kariyar nau'i, kuma take tunkudawa zuwa jima'i don nufin jin dadi; ta dukkan bangarorinta biyu na halayya da `yan Adamtaka tana tsayawa ne a bisa asasin kauna, jin kai da samar da natsuwa.

Da wannan AIkur'ani ya dauki mace a matsayin tushen natsuwa ta hanyar tabbacin hankali da na zamantakewa ga namiji da rayuwar zamantakewa baki dayanta; wannan kuwa saboda kosar da rai daga son wani jinsi da jaraba ta jiki daga gare shi, suna haifar da kawar da damuwar rai da na zuciya, da cika irin faragar da rai din ke da shi, da sarrafa karfin bukatar jima'i da halayya don tabbatar da daidaici ga jinsosin biyu da ke tsaye a kan asasin cika ta hanyar gamammiyar dokar auratayya ta halitta.

Daga nan nauyin da ya rataya a wuyan mace wajen gina rayuwar al'umma mikakkiya kuma mai lafiya ta jiki da zamantakewa ke iyakantuwa; saboda ita ce mabubbugar natsuwa, kauna, tausayi da jin kai cikin rayuwar zamantakewa.

2-Sanayya: Abu na biyu da ke sa mutum hada rayuwar zamantakewa, shi ne ka'idar nan ta sanayya tsakanin

mutane, abin da ke tsaye a bisa asasin nan na jin son zaman tare wanda masana falsafa ke nunawa da cewa: 'Mutum mai zaman tare ne bisa dabi'a".

Jarabce-jarabce na halayya da zamantakewa sun tabbatar da cewa mutum ba ya jin tabbas da kwanciyar hankali, kuma mutuntakarsa ba ta cika sai da zamantakewa da rayuwa tare da wasu. domin shi yana da matsananicyar bukata ta rai kuma mai Zurfi zuwa ga wasu, saboda haka ne ma Allah Ya fad'i cewa: ".-don ku san juna"; kalmar sanin juna na nuni ne ga boyayyen abin da ke tura mutum zuwa zamantakewa da hada al'ummar dan Adam.

3-Musayar amfanoni: Sababi na uku daga sabubban gina al'umma shi ne musayar amfanoni na abin duniya dabam-dabarn. Hakika Allah Ya so daidaikun mutane su sami cika da irin karfi da kwarewarsu ta tunani, jiki da hankali, kuma wannan cika na tabbata ne ta hanyar musayar amfanoni tsakanin daidaiku.

Kowane mutum -shi kadai- yana da bukatu da wasu abubuwa da yake nema masu yawa, kuma ba ya iya samar wa kansa da su duka; don haka yana bukatar wasu, su ma suna da bukata da shi, wannan sabani cikin kwarewa wanda daga gare shi ne ake samun sabani cikin nau'o'in abubuwan da ake samarwa da hidimomin da mutum ke iya yi ga wasu, da musayar wadannan abubuwa da amfanoni da hidimomi don biyan bukatu, shi ne wanda AIkur'ani mai girma ya yi maganarsa da cewa:­



back 1 2 3 4 5 6 7 next