Hukunce-hukuncen Soyayya



k- Wanda ya tsoratar da kai duniya

285. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: kada ka kaunaci (abotar) wanda ya guje ka[59].

l- ‘Yan Duniya

286. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ‘yan’uwan duniya soyayyarsu tana yankewa saboda saurin yankewar dalilanta[60].

287. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Kada ka yawaita abokan duniya; domin su idan sun gajiya sai su koma makiya. Misalinsu kamar wuta ce da yawanta yake kuna, kadan dinta yake amfani[61].

M- Wanda Ba Don Allah Yake So Ba

288. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka guji duk wanda soyayyarsa ba don Allah ba ce; domin soyayyarsa zargi ne, kuma abotakarsa shu’umi ce[62].

289. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Dukkan wata soyayya da aka gina ta ba don Allah ba to bata ce, kuma ba zai yiwu ba a dogara da ita[63].

290. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Ba a fatan son wanda ba shi da addini[64].

N- Tattararrun Bayanai Gaba Daya

291. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: babu alheri ga abotar wanda yake da dabi’u guda shida; idan ya yi maka zance sai ya yi karya, idan ka yi masa magana sai ya karyata ka, idan ka aminta da shi sai ya ha’ince ka, idan ka rike masa amana sai ya tuhume ka, idan ka yi masa ni’ima sai ya yi butulci, idan ya yi maka wata ni’ima sai ya yi maka gori[65].

292. Daga Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: Imam Ali dan Husain (A.S) ya ce da ni: ya kai dana, duba biyar kada ka yi abota da su, kada ka yi magana da su, kada ka yi abota da su a wata hanya. Sai na ce: ya baba su waye?

Sai ya ce: kada ka yi abota da makaryaci; domin shi kamar sururi ne; yana kusanto maka nesa yana kuma nesanta maka kusa. Kada ka yi abota da fasiki; domin shi zai iya sayar da kai da loma daya ko kasa da haka. Kada ka yi abota da marowaci; domin shi yana kaskantar da kai a game da dukiyarsa lokacin da kake bukata zuwa gareshi. Kuma na hana ka abota da wawa; domin shi yana son ya amfane ka sai ya cutar da kai. kuma na hana ka abota da mai yanke zumincinsa domin ni na same shi abin la’anta ne a cikin littafin Allah a wurare uku: Ubangiji madaukaki ya ce: “shin kuna fatan idan kuka juya baya ku yi barna a bayan kasa ku kuma yanke zumuncinku. Wadannan su ne wadanda Allah ya la’ance su kuma ya kurumtar da su kuma ya makantar da ganinsu”[66]. Kuma ya ce: “Su ne wadannan da suke warware alkawarin Allah bayan kulla shi, kuma suke yanke abin da Allah ya yi umarni a sadar da shi, kuma wadannan la’anar Allah tana kansu kuma suna da mummunan gida”[67]. Kuma ya fada a surar bakara: “Wadannan da suke warware alkawarin Allah bayan kulla shi kuma suke yanke abin da Allah ya yi umarni a sadar kuma suke barna a bayan kasa, wadannan su ne masu hasara” [68].[69]

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next