Hukunce-hukuncen Soyayya



f- Masu Shiryarwa Ga Alheri

246. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafificin abokai shi ne wanda yake shiryar da kai ga alheri[14].

247. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafificin abokai shi ne wanda yake taimakawa a kan biyayya[15].

g- Masu Ambaton Allah

248. Daga ‘Yan’uwa daga Hasan: suka ce: ya ma’aikin Allah, wane ma’aboci ne ya fi? Sai ya ce: ma’abocin da idan ka tuna Allah madaukaki sai ya taimaka maka, idan ka manta shi sai ya tuna maka. Sai suka ce ya ma’aikin Allah! ka shiryar da mu game da mafifitanmu domin mu rike su ma’abota majalisinmu? Sai ya ce: su ne wadanda idan aka gan su sai a tuna Allah[16].

h- Talakawa

249. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: da Abuzar, na umarce ka da son miskinai da zama da su[17].

250. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: na umarce ku da son miskinai, musulmai, domin hakika duk wanda ya wulakanta su ya yi musu girman kai to ya kaskantar da addinin Allah, kuma Allah yana mai wulakanta shi, kuma mai kinsa, kuma hakika babanmu ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce: “Allah ya umarce ni da son miskinai; musulmai (daga cikinsu). Ku sani cewa; wanda ya wulakanta wani daga muslumi to zai hadu da Allah yana kinsa kin da zai sanya mutane su ki shi, kuma Allah shi ne ya fi komai tsananin ki. Ku ji tsoron Allah game da ‘yan’uwanku musulmi miskinai; ku sani hakika suna da hakki a kanku na ku so su; hakika Allah ya yi umarni da sonsu, wanda kuwa bai so wanda Allah ya yi umarni da sonsa ba, to hakika ya saba wa Allah da manzonsa kuma idan ya mutu a hakan to ya mutu yana daga cikin halakakku[18].

i- Mata

251. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Son mata yana daga dabi’un annabawa (A.S)[19].

j- Miji da Mata

252. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: a game da kissar nan ta Haula’u: ya ke Haula’u! namiji yana da hakkin mace ta lizimci gidansa, kuma ta so shi, ta kaunace shi, ta tausaya masa[20].

253. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: fadin miji ga mace: hakika ni ina son ki, to ba ya fita daga zuciyarta har abada[21].

k- Yara

254. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku so yara, ku tausaya musu, idan kun yi musu alkawrin wani abu, to ku cika musu; ku sani su ba su sani ba, sai dai ku ne kuke ciyar da su[22].

255. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Musa dan Imrana ya ce: ya Ubangiji, wane ayyuka ne suka fi gunka? Sai ya ce: son yara; hakika ni na dora su kan kadaita ni, kuma hakika tarayyarsu ina shigar da su aljannata da rahamata[23].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next