Masu Hana Soyayya



4 / 2

Tattararrun aibobin soyayya

146. Daga Manzon Allah (S.A.W) idan ka so mutum, kuma ba ka jayayya da shi, ba ka kusantarsa, ba ka nuna shi, kuma ba ka tambaya game da shi; to ya kusata ne ya samu wani makiyi da zaka yarda da shi, sai ya ba ka labarin abin da ba shi da shi, sai ya raba tsakaninka da shi[30].

147. Imam Ali (A.S) ya ce: Ka guji jiji-da-kai, da mummunar dabi’a, da karancin hakuri; ka sani ba yadda za a yi ka samu aboki da wadannan dabi’u uku, kuma mutane ba zasu gushe suna guje maka ba[31].

148. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: idan wani mutum ya ce da dan’uwansa kai tir, to abin da yake tsakaninsu na kauna zai yanke, kuma idan ya ce: kai makiyina ne, to dayansu ya kafirta, idan kuwa ya tuhume shi to sai imani ya narke a zuciyarsa kamar yadda gishri yake narkewa a ruwa[32].

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari

Hafiz Muhammad Sa’id Kano

hfazah@yahoo.com


[1] Nahajul balaga: huduba: 113.

[2] Gurarul hikam: 8773.

[3] Gurarul hikam: 9178.



back 1 2 3 4 5 6 7 next