Masu Hana Soyayya



Masu Hana Soyayya

4 / 1

Aibobin Soyayya

a- Bakar Zuciya

117. Imam Ali (A.S) ya ce: hakika ku ‘yan’uwan ne na addinin Allah, ba wani abu ya raba ku ba sai bakar zuciya da mugun nufi, kuma kuka kasance ba kwa daidaitawa ba kwa nasiha, ba kwa kyauta, kuma ba kwa soyayya[1].

b- Mummunan hali

118. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda dabi’arsa ta munana to masoyinsa da abokinsa zasu ki shi[2].

119. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda dabi’arsa ta munana, to ya rasa aboki da amini[3].

c- Bin Aibobi

120. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda yake bin boyayyun aibobin mutane, to Allah zai haramta masa son zukata[4].

 121. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: wanda ba ya abota sai da mai aibi, to abokansa zasu karanta[5].

d- Nisantar Mutane

122. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya yi nesa da abokinsa, soyayyarsa ta yanke[6].

123. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya nisanci ‘yan’uwa a kowane laifi, to abokansa zasu karanta[7].

e- Jayayya Da Mutane

124. Babu soyayya tare da yawan jayayya[8].

f- wauta

125. Imam Ali (A.S) ya ce: Ka nisanci wawa; domin shi yana dimautar (nisantar) da abokai[9].



1 2 3 4 5 6 7 next