Kiyayya Don Allah



40. Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: Hakika shedan yana kawo rudu tsakanin muminai matukar dayansu bai bar addininsa ba, idan kuwa suka yi haka sai ya kwanta a kishingede a kan keyarsa ya mike kafafuwansa, sannan sai ya ce: na rabauta. Allah ya yi rahama ga mutumin da ya daidaita tsakanin masoya biyu, ya ku tarayyar muminai, ku hadu ko tausaya wa juna[15].

41. Hilyatul auliya: imam Hasan (A.S) ya ce; wani mutum ya zo wajen Annabi (S.A.W) zuwa ga ahlussuffa, sai ya ce: yaya kuka wayi gari? Sai suka ce: da alheri. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku ne masu alheri a yau, amma idan dayanku ya samu kabaki, aka tafiyar da wancan (halin wato; kuka samu yalwar duniya) dayanku ya rufe gidansa kamar yadda ake rufe ka’aba. Sai suka ce ya ma’aikin Allah (S.A.W) zamu samu hakan alhalin muna kan addininmu? Sai ya ce; haka ne. sai suka ce; ashe kenan a wannan lokacin mun fi yin aikin alheri, mu yi sadaka mu kuma ‘yanta bayi. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ba haka ba ne, a yau kun fi yin alheri; domin ku idan kuka same ta, to zaku yi hassada ku yanke wa juna, ku ki juna[16].

42. Imam Ali (A.S) ya ce; kada ku yawaita zargi; hakika yana gadar da gaba da mugun kulli, kuma yana kai wa zuwa ga kiyayya, kuma yana yawaita mummunar dabi’a[17].

43. Daga gareshi (A.S); -a cikin wasiyyar da ya yi wa dansa Hasan (A.S)- Raha tana haifar da mugun kulli (kuduri: wato; gaba)[18].

44. Daga gareshi (A.S) ya ce: Jafa’i shi ne asalin farkon yanke juna[19].

45. Daga gareshi (A.S) ya ce: yin kage kan juna shi ne asasin yanke wa juna[20].

46. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Abubuwa uku suna kawo gaba: munafunci, da zalunci, da jiji-da-kai[21].

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari

Hafiz Muhammad Sa’id Kano

hfazah@yahoo.com



back 1 2 3 4 5 next