Kiyayya Don Allah



35. A Littafin Kafi; daga murazim dan Hakim: ya ce; wani mutum daga sahabbanmu da ake yi masa lakabi da shalkan ya kasance gun Abu Abdullah (A.S), ya kasance ya sanya shi kan al’amarin ciyarwarsa, ya kasance maras kyawun halaye, sai ya kaurace masa. Sai wata rana Imam (A.S) ya ce da ni: ya kai murazim, kana kuwa yi wa Isa (sunan shalkan kenan) magana? Sai na ce: E. sai ya ce: ka kyauta, (domin) babu alheri cikin kauracewa[9].

2 / 3

Hani Ga Kauracewa Sama Da Kwanaki Uku

36. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: bai halatta ba ga musulmi ya kauracewa dan’uwansa sama da kwanaki uku, kuma mai rigon (sulhu shi ne zai yi rigo) zuwa ga aljanna[10].

 Daga gareshi (A.S) ya ce: dukkan musulmai da suka kaurace wa juna, sai suka zauna a haka sama da kwanaki uku ba su yi sulhu ba, sai sun kasance sun fita daga musulunci, kuma ba su da wata soyayyar Allah da ta rage musu, kuma duk wanda ya riga zuwa magana ga dan’uwansa shi ne zai yi rigo zuwa aljanna ranar hisabi[11].

2 / 4

Cutarwar Yankewa Juna

38. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: -a cikin wata wasiyya da ya yi wa Abuzar- Ya Abuzar, na hana ka kaurace wa dan’uwanka mumini, ka sani aiki ba ya karbuwa tare da kauracewa[12].

39. Daga gareshi (S.A.W) ya ce: “Ana bude kofofin aljanna ranar litinin da ranar alhamis, sai a gafartawa duk wani mumini da ba ya shirka da Allah da wani abu, sai mutumin da ya kasance tsakaninsa da dan’uwansa akwai kiyayya, sai a ce: ku jira wadannan har sai sun shirya, ku jira wadannan har sai sun shirya[13].

2 / 5

 masu Jawo Gaba Da Kiyayya

Kur’ani:

“Hakika kadai shedan yana son ya haifar da gaba da kiyayya tsakaninku ne a cikin giya da caca, kuma ya kange ku daga barin ambaton Allah kuma daga barin salla, shin ba kwa daina ba”[14].



back 1 2 3 4 5 next