Addu’a Ibada ceKuma sun sanya wannan daga cikin cika alkawura ga Imamai, domin ga kowane imami akwai alkawarinsa a kan wuyan mabiyansa, kuma ziyartarsu tana daga mafificin cika alkawari, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da gaskata abin da suka kwadaitar a kai, to zasu kasance masu cetonsa a ranar lahira[2]. Akwai fa’idoji masu yawa na Addini da zamantakewa a cikin ziyartar kaburbura da suka sa Imamanmu himmantuwa da ita, domin bayan dada karfin soyayya da mika wuya da kauna tsakanin imamai da mabiyansu, hada da sabunta ambatonsu da tuna kyawawan dabi’unsu, da jihadinsu a tafarkin gaskiya, tana kuma hada musulmi daban-daban wadanda suke warwatse a waje daya domin su san juna, kuma ta dasa ruhin mikuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu, da yankewa zuwa gare shi da bin umarninsa, tana cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma’anonin addu’o’in ziyarorin da suke cike da fasaha wadanda aka samo daga Ahlul Baiti (AS), tare da koya musu tsarkin Musulunci da sakonsa, da abin da ya wajaba a kan musulmi na daga dabi’u madaukaka, da kaskan da kai ga mai tafiyar da al’amuran halitta (S.W.T), da gode wa ni’imominsa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu’o’in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya gabata. Wasunsu ma suna dauke da sama da haka, kuma mafi daukakarta kamar ziyarar “AminulLahiâ€‌ wacce take ziyara ce da aka rawaito daga Imam Zainul Abidin (A.S) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa imam Ali (A.S). Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito suke fahimtar da matsayin imamai (AS) da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya, da daukaka kalmar Addini da kadaitarsu ga ibadar Allah (S.W.T), ga shi kuma sun zo da salon larabci mai fasaha madaukakiya, da ma’anoni masu sauki wadanda kowa yake iya fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma’anonin tauhidi masu zurfi, da addu’a, da yankewa zuwa gare shi madaukaki. Hakika tana daga cikin mafi ingancin ladubban Addini bayan Kur’ani mai girma da Nahjul Balaga da kuma addu’o’in da aka ruwaito daga garesu (AS), domin a cikinta akwai takaitaccen bayanin sanin Imamai (AS) game da abin da ya shafi sha’anin Addini da gyaran zuciya a dunkule. Sannan a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da samuwar wadannan dabi’u na Addini madaukaka, wanda ya hada da daukaka tsarkin ruhin musulmi, da yaduwar tausasawa ga fakiri, da iya zamantakewa da al’umma, da son cudanya da jama’a, domin daga ladubbanta akwai abin da ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin ginin makabartar domin ziyartarsa. Daga nan kuma akwai abin da ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar, da kuma bayan ziyarar, da mu a nan zamu bujuro da sashen wadannan ladubban domin fadakarwa kan manufarta da muka ambata: 1- Daga ladubbanta, mai ziyarar ya yi wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka, fa’idar wannan kuwa cikin abin da muka fahimta a fili take, ita ce mutum ya tsarkake jikinsa daga dauda, domin ya kubutar da shi daga rashin lafiya da cututtuka, kuma domin kada mutane su gundara[3] da warinsa, ya kuma ya tsarkake kansa daga kazanta. Hakika ya zo a cikin hadisai cewa; mai ziyara ya karanta wannan addu’a bayan ya kare wanka domin fadakar da shi game da wadancan manufofi madaukaka, sai ya ce: “Ya Allah ka sanya mini haske da tsarki tare, da kuma tsari mai isarwa ga dukkan cuta da ciwo da dukkan aibi, kuma ka tsarkake zuciyata, da gabobina, da kasusuwana, da namana, da jinina, da gashina, da fatata, da bargona, da kashina, da kuma abin da kasa ta dauke shi daga gare ni, kuma ka sanya mini halarta ranar bukatata da fakirancina da talaucina.â€‌ 2- Ya sanya mafi kyawu kuma mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa da tsaftatattun tufafi a taron jama’a abu ne da mutane suke so wa junansu, kuma yake kusantar da su ga junansu, tare da kara musu daukaka da jin daukaka a bukin da suke halartarsa. Daga abubuwan da suka kamata mu jawo hankali garesu a wannan koyarwa su ne, ba a wajabta wa mai ziyara sanya mafi kyawun tufafi baki daya ba, a’a, sai dai ya sanya mafi kyawun abin da zai iya, domin ba kowa ne zai iya yin haka ba, kuma akwai takurawa ga talakawa, al’amarin da tausayawa ba ta bukatar a yi haka, sai ya zamanto ya hada tsakanin wannan tarbiyya da abin da ya kamata na kawa da kuma kiyaye halin talaka da mai raunin hali. 3- Ya sanya turare matukar yana da shi, wannan fa’idarsa tamkar ta sanya sababbin tufafi ce. 4- Ya yi sadaka ga fakirai da abin da ya saukaka gare shi, kuma fa’idar sadaka a irin wannan al’amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimaka wa gajiyayyu, da kuma karfafa ruhin tausasawa gare su.
|