Aure A Shari'ar Musulunci



1)    Auren Da'imi.

2)    Auren Mutu'a.

1)    AUREN DA'IMI, (auren da Bahaushe kece masa auren mutu-ka-raba) wanda shine madaukakin auren da Musulunci ya gina. Wannan shine bangare na farko da Shari'a ta yarda da shi a Babin aure.

2)    AUREN MUTU'A, (Auren da ake kullawa abisa yarjejeniya zuwa wani kayyadajjen lokacin da zai kare a rabu), wanda shine makariyar dake kare mutum daga afkawa ga Zina, yayin da auren Da'imi ya gagari mutum. Ko kuma akwai damar, amma sai dai mutum yayi abisa zabin kansa, wanda hankali da Shari'a sun yarda da aikata hakan.

Hakika auren Mutu'a yana tafiya Sahu bayan Sahu tare da ainihin auren Da'imi ta bangaren tafiyar da Sha'awa abisa tafarki na Halas. Da kuma kiyaye Nasaba (Dangi) da kariya kada ta cudanya da gurbata, da kare Matsayi da Mutunci na dukkanin Al'umma. Kuma a bangare daban yana da rangwame wanda bai shafi ainihin gundarin auren (Da'imi) ba (Kamar Sutura, Gidan zama na dindindin). A auren Mutu'a akwai Daurin aure, da  bada Sadaki, da kuma yin Idda, sannan da ayyanannen lokaci (dole ne ayyana lokaci yayin daura shi, wanda idan lokacin ya cika to wannan auren ya kare). Sannan babu Gado da "Nafakah" (wato wasu wahalhalu da suka shafi yau da kullum, kamar Ciyarwa, Sutura, da sauran su).

Wannan nau'i na aure tabbatacce ne ingantacce a fuska ta Shari'a, da Nassin Kur'ani da Sunna mai tsarki. Babu wani daga cikin Musulmi da ya saba akan halascin sa a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi). Abinda kadai ya faru ga al'amarin mutu'a shine Halifa Umar dan Haddabi ya hana yin sa kuma yake azabtar da duk wanda aka samu yanayi (amma idan mutum ya zamanto bai fito daga wani babban Dangi ba). Don hakane Makarantar Khulafa'u (Ahlus-sunna, masu riko da dayan Mazahabobi hudu, MALIKIYYA, HANAFIYYA, SHAFI'IYYA DA HANBALIYYA, da wasun su masu bin gundarin ra'ayin kansu a tsakanin Ayoyi da Hadisai) ke bin wannan hani da hujjarsu ta bin aikin Sahabi, (ba bin aikin Annnabin da aka aiko musu ba). Daga cikinsu akwai wadanda suka sanya wai wannan aure akan an shafe shi daga baya, sai dai har yanzu ba muga Ayar da ta shafe shi ba.

Don haka a wajen tabbatar da ingancinsa, an fadi zantuka da dama akansa, a ciki akwai: Haramci da Hanin sun faro ne daga zamanin Fiyayyen Halittu (Sallallahu alaiHi wa Alihi) kansa, kuma wai Kur'ani ya shafe Ayar halascin auren Mutu'a. Don haka abisa tabbatar da hakika na menene gaskiya a wannan bigire na Shari'a muhimmi, ba makawa sai mun bi takan wadannan maganganu guda uku:

·        Magana ta daya: Auren Mutu'a cikin Kur'ani da Sunna.

·        Magana ta biyu: Shin an shafe hukuncin Auren Mutu'a da gaske?

·        Magana ta uku: matsayin Sahabbai da Tabi'ai akan Auren Mutu'a.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next