Mene ne Auren Mutu'a



"To ku sake su da Iddar su" (Addalak: 1)

Suna kawo cewar al'amarin Idda a wannan Aya ya shafe hukuncin auren Mutu'a wacce ita babu Saki babu Idda a cikinta.

Jawabi:

Hakika auren Mutu'a bai kasance ance babu Idda ba, Allahumma sai dai ace babu Saki a cikinsa. Idan muka komo kan aure a Musulunci ya kasu kashi biyu ne: Da'imi da Munkadi'i (Mutu'a), don haka zai kasance kenan ita Ayar Saki tana Magana ne kadai akan auren Da'imi ba Mutu'a ba. Domin alakar da take dawwamammiya (mutu-ka-raba) ce, itace take bukatar sanarwa akan kawo karshen alakar yayin faruwar wani dalili na hadari ayyananne. Amma alaka wacce take "Mu'akkita" wacce daman tuni anyi mata lokacin da zata kare bata bukatar wannan ambatawar, tana karewa ne yayin da lokacin da aka debar mata ya kare da yanayi na nan take. A irin wannan yanayi ne sai Ayar Saki ta zamo an barta har abada, babu wani abin kulawa a cikin ta game da auren Mutu'a, balle har ma takai ga ta zamo ta janyo shafe ta.

Akwai Magana ta uku wacce ake cewa auren Mutu'a shafaffene saboda babu Gado a ciki.

Wanda maganar da ta gabata ta isa jawabi kan wannan. Kamar yadda har wala iyau yake cewar, buyar wasu daga cikin Kaya baya nuni akan rashin gurin da aka ajiye su Kayan. Matar da take ballagaza wacce bata da kamun kai babu "Nafakah" (Dawainiyar yau da kullum, kamar Sutura, Ci da Sha, da sauran su) akanta, tare da cewar an hana mata wannan "Nafakah" din, amma kuma duk da hakan tana nan a matsayinta na matar aure, kuma sauran hukunce-hukunce na gudana akanta da abubuwan da suka shafi aure.

Hakanan matar da take "Kitabiyya" (wacce take bin wani Addinin da aka saukar ba Musulunci ba, kamar Kiristanci, Yahudanci) idan ta auri Musulmi, bazata gaje shi ba, kuma duk da hakan tananan dai a matsayin ta na matarsa, da sauran abubuwa da hukunce-hukunce.

Sannan kuma ma dai yawan maganganu akan shafe hukuncin auren Mutu'ar kansa dalili ne dake nuna rashin tabbatar shafewar.. Kuma har wala iyau sassabawar su a cikin shi kansa lokacin da aka shafe din na kara shaida hakan.

Misali:

·        Wasunsu sukace: An shafe hukuncin ne, kuma Manzon Girma (Sallallahu alaiHi wa Alihi) ya hana ne a lokacin shekarar Yakin Khaibara.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next