'Yan'uwantaka Da Daidaitawa



Haka nan haramcin bambanta sallama tsakanin fakirin musulmi da mai kudi.

An ruwaito Imam Ridha (a.s) yana cewa: “Wanda ya hadu da musulmi fakiri sai ya yi masa sallama sabanin irin wanda yake yi wa mai kudi, zai hadu da Allah Madaukakin Sarki Ranar Lahira alhali yana cikin fushi[2]”.

Haka nan cin mutumcin mumini fakiri saboda talaucinsa.

Daga Imam Sadik (a.s) daga Iyayensa (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w.a) cikin wani hadisi yana cewa: “Wanda ya kaskantar da fakirin musulmi lalle ya kaskantar da hakkin Allah, to lalle Allah Zai kaskantar da shi Ranar Lahira, sai dai in ya tuba[3]”.

Daga gare shi yana cewa: “Wanda ya wulakanta mumini da ci masa mutumci saboda rashin abin hannu da talaucin da ke fama da shi, Allah Zai tayar (bayyanar) da shi a kawukan halittu[4]”.

Daga Imam Ridha (a.s) daga Iyayensa (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “……..har zuwa mutuwa: cin abinci a kas tare da bayi……sanya sufi da sallama ga yara[5]”.

Abin da muka ambata yayi bayanin kan daidaito tsakanin muminai yayin aure yana tabbatar da wannan hakika a fili.


[1] . Wasa’il al-Shi’a 8:437, babi na 33 hadisi na 1.

[2] . Wasa’il al-Shi’a 8:442, babi na 36, hadisi na 1.

[3] . Wasa’il al-Shi’a 8:588, babi na 146 hadisi na 4.

[4] . Wasa’il al-Shi’a 8:591, babi na 147, hadisi na 4.

[5] . Wasa’il al-Shi’a 8:441, babi na 35, hadisi na 1.

 



back 1 2