Ladubban Zamantakewa



Akwai ruwayoyi da aka ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) da suke magana kan mike kafa yayin zama, wanda suke nuni da halalcin hakan idan har saboda hutu ne na dan wani lokaci, saboda hadisin da aka ruwaito daga Aliyu bn Husain (a.s) da ke nuni da hakan inda ya ke cewa: “Lalle na yi irin wannan zama ne saboda gajiya[8]”.

A fili yake cewa wadannan yanayi guda uku na zama suna nuni da ladubban zama ne, a bangare guda kuma da tattalin waje, gwargwadon yanayin zamantakewa da yanayi na wancan lokacin.

Tawali’ua Wajen Zama

e) – tawali’u a wajen zama, wato shi ne mutum ya zauna a karshen waje (inda ya fi kusa da shi) yayin shigowarsa, an ruwaito Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Duk wanda ya yarda da wajen zama ba tare da nuna girman kai ba, Allah da mala’ikunSa za su ci gaba da yi masa salati har ya tashi daga wajen[9]”.

Hakan na daga cikin abin da aka ruwaito kan dabi’un Ma’aikin Allah (s.a.w.a), yayin da aka ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance idan ya shigo gida (waje) ya kan zauna a (karshen) wajen da yafi kusa da shi[10]”.

A nan gaba bayani kan mustahabi ne mutum ya fuskanci alkibla yayin zama a nan gaba, da kuma rashin ingancin fuskantar rana a yayin zama, saboda abubuwan da suke tatttare da hakan na ruhi da na duniya[11].

NemanRahama ga Mai Atishawa

Na Biyu: Neman gafara ga wanda ya yi atishawa, wato a ce wa mutumin da ya yi atishawa: “Yarhamukallah”, shi kuma sai ya ce: “Yahdi kumullah wa yaslihu balakum” ko kuma wata addu’a makamanciyar hakan, misali: “Yagfirullah lakum wa yarhamakum” ko “Yagfurullah lana wa laka”, wannan na daga cikin ladubban da Ahlulbaiti (a.s) suna jaddada da kwadaitarwa kansa suna masu koyi da Ma’aiki (s.a.w.a).

An ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Daga cikin hakkin musulmi a kan dan’uwansa musulmi da ya yi masa sallama idan ya hadu da shi, ya tafi gaishe shi idan ba shi da lafiya, yayi masa fatan alheri idan ba ya nan, yayi nema masa rahama idan ya yi atishawa, wato idan ya ce: Alhamdu lillah Rabbil alamin la sharika laHu, sai ya ce: Yarhamukallah, sai ya amsa masa da cewa: Yahdi kumullah wa yaslih balakum, sannan ya amsa masa idan ya gayyace shi (ko kuma ya nemi taimakonsa), ya tafi jana’izarsa idan ya mutu[12]”.

Kamar yadda aka ruwaito daga gare shi (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Idan mutum ya yi atishawa ku nema masa gafara ko da kuwa yana bayan jazira ne[13]”.

A wannan babin akwai ladubba da koyarwa da dama, misali: wanda ya yi atishawa ya ce: alhamdu lillah, an so ya kara da salati ga Annabi da Alayensa (a.s), ya maimaita nema masa rahama har zuwa sau uku, da kuma halalcin yin hakan (neman rahamar) ga kafirin amana da dai sauran abubuwa[14].

LadubbanMagana (Tattaunawa)

Na Uku: magana da ladubban da suke tattare da ita, a baya mun yi ishara da wasu ladubban, kamar lizimtar kiyaye sirri da amana a cikinta, saboda “akwai amana a wajen zama”, ba ya halalta ga wani ya fadi maganar da dan’uwansa ya gaya masa wanda kuma yake boyewa har sai da izininsa, sai dai idan ambatonsa da alheri ne da dai sauran ababen da aka kebance[15].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next