Hukunce-hukuncen Shari'a



Daga Ja’afar bn Muhammad daga Babansa (a.s) yana cewa: “Idan wani daga cikinku ya shiga gidan dan’uwansa yayin wata tafiya, to ya zauna inda mai gidan ya umarce shi, saboda mai gidan shi ya fi sanin sirrin gidansa sama da wanda ya shigo[10]”.

2 – Haramcin makirci, hassada, algishshu da ha’inci.

Daga Aliyu bn Musa Ridha (a.s), daga Babansa daga Iyayensa (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Musulmi ba ya makirci da rudi, don ni na ji Mala’ika Jibrilu yana cewa: (mai) makirci da rudi na wuta, sai ya ce: Ba ya daga cikinmu wanda ya cuci musulmi, ba ya daga cikinmu wanda ya ha’inci musulmi. Daga nan sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Hakika Jibrilu ya sauko daga wajen Ubangijinsa zuwa gare ni yana mai cewa: Ya Muhammadu! Ina gargadinka da kyawawan dabi’u, don mummunar dabi’a tana gusar da alherorin duniya da na lahira. Ku sani wanda ya fi kama da ni daga cikinku shi ne wanda ya fi kyawawan dabi’u[11]”.

An ruwaito Imam Ali (a.s) yana cewa: “Da ba don cewa (mai) makirci da rudi na wuta ba, da na kasance mafi makircin mutane[12]”.

3 – Haramcin karya da dukkan nau’ointa a ko ina, musamman ma cikin mu’amalar mutum da sauran mutane, in dai ba wajajen da aka kebance ba kamar wajen kyautata tsakanin mutane biyu kamar yadda muka ambata a baya.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Allah Madaukakin Sarki Ya sanya wa sharri makulli, Ya sanya abin sha (giya) mabudin wannan makulli, karya ta fi giya sharri[13]”.

An ruwaito Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Ya kamata ga mutum musulmi ya nesanci ‘yan’uwantaka ta karya, saboda yawan karya ya kan sa ko da ya zo da gaskiya ba za a yarda ba[14]”.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Aliyu bn Husain (a.s) ya kasance ya kan gaya wa dansa: ka ji tsoron karamar karya ko babbarta da gaske ko da wasa, saboda idan ya yi karya karamin abu zai yi kan babba. Ba ku san cewa Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Bawa ba zai ci gaba da fadin gaskiya ba har sai Allah Ya rubuta shi cikin masu gaskiya, kamar yadda bawa ba zai ci gaba da karya ba, har sai Allah ya rubuta shi cikin makaryata[15]”.

Daga Ali Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Karya ko da gaske ko da wasa ba ta inganta, haka nan mutum ya yi alkawari wa dansa ya ki cikawa. Lalle gaskiya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, fajirci kuwa na shiryarwa ne zuwa ga wuta. Wani ba ya ci gaba da karya har sai an ce: ya yi karya ya zama fajiri, waninku ba zai ci gaba da karya ba har sai ya rage ba shi da sauran wajen gaskiya ko da kamar kan allura ne[16], daga nan za a sanya masa sunan makaryaci a wajen Allah[17]”.

4 – Haramcin mutum ya zamanto ma’abucin fuska da harshe biyu cikin alaka ta zamantakewa.



back 1 2 3 4 5 6 next