Yin Kuka



Kuka A Kan Rabuwa Da Masoya

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Bakin ciki kuwa yayin da mutum ya rasa wani nasa ko abokansa, wani abu ne wanda yake kunshe a cikin halittar mutum. A lokacin da wani yake cikin musibar rashin wani nasa ko wanda ya sani, mutum zai kasance cikin bakin ciki, ba tare da ya sani ba hawaye zasu zubo daga idanunsa. Zuwa yanzu ba a samu wanda yake inkarin wannan hakikar ba ta yadda ya zamana mutum da gaske yake yana inkarin hakan. Babu shakka a bayyane yake cewa musulunci addini ne wanda yake ya dace da fitra da halittar mutum, sannan ba tare da sabawa halittar mutum ba ya tsara masa hanyar rayuwa: “Ka tsayar da fuskarka ga addini tsarkake na Ubangiji, halittace wacce Allah ya halatta mutum a kanta”[1].

Babu shakka ba zai yiwu ba ya zamana addinin da yake na duniya ya zo kuma ya hana mutane kuka yayin da suka rasa wani nasu, matukar dai ba zai haifar da hushin ubangijin ba yin hakan.

Bincike a kan tarihi ya tabbatar mana da cewa Manzo (s.a.w) da sahabbansa da tabi’ai dukkan sun yi rayuwarsu ne a kan dabi’a ta “yan adamtaka. A nan zamu kawo wasu abubu na tarihi a matsayin sheda a kan abin da muka fada kamar haka:

Manzo (s.a.w) yayin da dansa Ibarahim ya rasu ya yi kuka a kan rashinsa, yana mai cewa: Idanuwa suna kuka zuciya tana konewa, babu abin da zamu fada sai abin da yake neman yardar Allah ne, ya Ibarahim mun yi bakin ciki a kan rabuwa da kai”![2]

Masu tarihi sun rubuta cewa: Lokacin da Ibrahim dan manzo yake cikin magagin mutuwa, sai Manzo ya shigo cikin gida, ya gan shi bisa cinyoyin mamarsa a rungume,. Sai Manzo ya karbe shi, ya kwantar da shi bisa cinyarsa sai ya ce:



1 2 3 4 5 next