Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 2



Sai Manzo ya ce masa lallai ka roki Allah da babban suna wanda idan aka kira sa da shi zai amsa, idan kuwa aka roke shi da shi zai bai wa mutum abin da ya nema. [1]

2-Ya zo a cikin wata addu’a Imam Bakir da Imam Sadik (a.s) suna cewa: “Ya Allah ina rokon ka da babban sunanka wanda ya fi kowane girma, mafigirma da daukaka wanda idan aka roke ka da shi domin kofofin da suke a kulle a sama ana so su bude zasu bude, sannan idan aka kira ka da shi domin fadada kofofin da suke kasa zasu fadada, kuma idan aka roke ka da shi domin samun sauki, za a samu saukin. “[2]

2-Kamun kafa Da Kur’ani

Daya daga cikin hanyoyin da ake kamun kafa da su domin neman kusanci ga Ubangiji shi ne mutum ya karanta Kur’ani, ta wannan hanyar sai Allah ya biya masa bukatarsa. A hakikanin gaskiya wannan nau’in kamun kafa, kamun kafa ne da ayyukan Ubangiji, domin kuwa Kur’ani maganar Allah ce wacce ta sauka a kan zuciyar Manzo (s.a.w)

Ahmad Bn Hambal ya ruwaito daga Imran Bn Husaini yana cewa: Na ji daga manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Ku karanta Kur’ani ku roki Allah da shi, kafin wasu gungun mutane su zo wadanda zasu roki mutane da shi.[3]

Idan muka lura da kyau a cikin wannan hadisi yana nuna mana wani abu, wannan kuwa shi ne, kamun kafa da duk wanda yake da girma da matsayi a wajen Allah wani abu ne wanda ya halatta, saboda mustahabbi ne a daren lailatul kadari mutum ya buda Kur’ani ya karanta ya roki Allah da shi tare da wannan addu’a kamar haka: “Ya Allah ina rokonka da wannan Kur’ani da abin da ka saukar a cikinsa, a cikinsa akwai babban sunanka da sunayenka kyawawa…

3-Kamun kafa Da Kyawawan Ayyuka

Kamar yadda muka ambata a farkon wannan Bahasi cewa idab mutum yana so ya cimma wani abu na rayuwar duniya ta hanyar hankalinsa ne zai gano ta wace hanya ce ya kamata ya bi domin ya cimma wannan abin da yake nema. Wato mutum ya san abin da ya dace ya aikata domin ya biya bukatunsa na rayuwa, misali kamar idan mutum yana jin yunwa ko kishirwa ya san cewa abinci ko ruwa zai sha don ya yi maganin wannan kishirwa da yunwar. Amma dangane da abin da ya shafi ruhi ko lahira, ba zai yiwu ba mutum ya iya gano hanyar da zai bi don ya cimma abin da yake so ya cimmawa, saboda haka a nan yana da bukatuwa zuwa Allah ko wakilinsa wanda zai gwada masa hanyar da ya kamata ya bi, sannan ba tare da jagorancinsa ba babu yadda zai yi ya isa zuwa ga hadafinsa, domin kuwa bin wata hanya wacce ba shari’a ba ce ta bayyana hakan zai zama bidi’a a cikin addini. Saboda haka musulmi dole ne a nan dangane da abin da ya shafi addini ya yi riko da abin da yazo a cikin Kur’ani da Sunna.

Kamun kafa da kyawawa kyawawa wanda shi ne nau’i na uku a cikin wannan Bahasi, a cikin Kur’ani an yi nuni da shi duk da cewa ba a bayyane ba ne kamar yadda ya zo a bayyana ne a cikin hadisai, bayaninsa kuwa atakaice shi ne, idan mutum ya aikata wani aiki domin Allah, yayin da mutum ya shiga wata matsala, yana iya ambatar wannan aikin da ya yi mai kyau domin Allah madaukaki ya yaye masa matsalar da ya shiga. Kai duk lokacin da mutum ya aikata wani aiki mai kyau yana iya rokon Allah da ya biya masa bukata da wannan aiki da ya aikata. Ga wasu abubuwa da suka zo a tarihi wadanda suke ba da sheda a kan hakan.

1-Annabi Ibrahim yayin da yake gina dakin ka’aba, ya roki Allah da ya sanya shi da dansa Isma’il su kasance masu biyayya ga Allah. Ga abin da Kur’ani yake cewa a kan haka: “A lokacin da Ibarahim shi da Isma’il suke daga ginin Ka’aba, sai suka ce ya Allah ka karba mana kai ne mai ji masani. Ya Allah ka sanya mu masu mika wuya gare ka, sannan daga zuriyar mu ka sanya su masu mika wuya a gareka, ya Allah ka koyar da mu ayyukan hajji, ka kuma karbi tubarmu, lallai kaine mai karbar tuba mai jin kai. “[4]Mun ga yadda annabi Ibarahim da dansa Isma’il suka yi kyakkyawan aiki na ginin dakin ka’aba, a wannan lokaci sai suka roki Allah wasu abubuwa kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next