Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan AllahSaboda haka nufin Allah ya yi rigaye a kan cewa duk da cewa dole ne mutum ya yi imani da cewa komai yana zuwa ne daga Allah, amma duk da haka mutum dole ne ya tanaji wasu abubuwa wadanda zasu kai shi zuwa ga cimma abin da yake nema. Wannan asali da ka’ida kuwa, tana gudana har da abubuwan da suka shafi shiryarwa da makamantansu, sakamakon haka ne Allah madaukai ya bai wa mutum wata halitta a cikin zatinsa wacce zata taimaka masa wajen yin imani da Allah, haka hankali, annabawa da malamai da masana da makamantan wannan, Allah madaukaki ya sanya su a matsayin wadanda zasu yi mana jagora domin mu samu shiriyar Ubangiji. Kamar yadda ya kasance a wasu wurare a cikin Kur’ani mai girma Allah yana bayyana cewa shiriya wani abu ne daga gare shi, kamar inda yake cewa: “Yana batar da wanda ya so yana kuma shiryar da wanda ya soâ€[8]. Sannan wani wurin yana cewa: “Lallai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciyaâ€. [9] Sannan babu karo da juna don an jingina shiryarwa zuwa ga dukkansu su biyun, wato asalin shiryarwa yana ga Allah, sannan Manzo wanda yake kamar sila ne na aiwatar da wannan aiki, babu laifi a jingina wannan aiki zuwa gare shi. Takaitaccen tunanin wasu wadanda suke aibata kasantuwar tasirin wasu halittu ya samu asali ne sakamakon rashin fahimta mai kyau a kan koyarwar Kur’ani mai girma kamar yadda suke ganinsa ya saba da azirtawar Ubangiji da kuma tawakkali da shi, don haka ne ba su iya fassara koyarwar Kur’ani ba da kyau kamar yadda ya kamata. Kasantuwar tasirin wasu daga cikin abubuwan halitta, sama ba ya karo da tawakkalli ko kadaita Allah a cikin tafiyar da al’amura, haka nan a cikin kadaita Allah a cikin ayyukansa. Domin kuwa a wajen mutum mai tauhidi wanda kuma yake da ilimi, dukkan wasu abubuwan da suke tasiri a cikin rayuwa suna yin wannan tasiri ne a karkashin inuwar Ubangiji da izininsa. Sannan yana ganin duk wani tasiri da yake a cikin duniya yana bayyana nufin Ubangiji wanda ba shi da iyaka wajen aikinsa kuma wanda ya halicci duniya baki daya. Sannan dangane da bukatun ruhi da na zahiri a wajen hakan, babu wani bambanci. Sakamakon haka ne Allah yake umurtar masu imani da su tashi domin su yi kamun kafa a wajensa inda yake cewa: “Yaku wadanda kuka yi imani, ku ji tsoron Allah, sannan ko nemi tsani zuwa gare shi, Kuma ku yi jihadi a tafarkin Allah ko kun rabautaâ€. [10] A nan dole mu yi bincike a kan ma’anar wannan tsani da aka ambata a aya ta sama me ake nufi da shi? Marubuta kamusun lugga sun bayani a kan yadda ake amfani da lafazin wasila cikin harshen larabci kamar haka: 1-Makami da matsayi: a wani hadisi Manzo (s.a.w) yana cewa: “Ku nema mini matsayi a wajen Allahâ€[11]
|