Rayuwa Bayan Mutuwa 3Ayoyin Kur’ani zasu yaye mana hijabi, yadda alakar mutane take da wadanda suke rayuwa a barzahu, saboda haka a nan zamu kawo wasu daga cikin wadannan ayoyi da suka yi bayani a kan haka, ta yadda zamu gane ya wannan alaka take tsakanin mu da wadanda suka tsallaka zuwa wata duniya ta hanyar gadar mutuwa, kuma ta yaya ne har yanzu alakarmu da su ba ta yanke ba. (Duk da cewa wannan al’amari koda bai hade kowane mutum ba, amma tabbas akwai wadanda suke da wannan alakar). 1- Salih (a.s) yana magana da ruhin mutanensa Ayoyin da suke ba da sheda a kan yadda mutane suke da alaka da mutanen da suka wuce, wannan aya mai zuwa tana nuna mana yadda Annabi Salih yake magana da mutanensa wadanda aka hallakar, yana cewa: “Suka soke taguwa suka saba umurnin ubangijinsu, sannan suka ce: Ya Salihu idan har kai annabi ne to ka zo mana da azabar da kake yi mana alkawari da itaâ€. “Sai girgizar kasa ta kama su sakamakon tsawar da Allah ya yi musu, suka wayi gari a cikin gidajensu a maceâ€. “A wannan lokaci sai ya nisance su, kuma ya ce musu yaku mutane lallai na isar muku da sakon Allah, sannan na yi muku nasiha amma ba ku son nasihaâ€.[1] A kula da kyau dangane da abin da wadannan ayoyi guda biyu suke magana a kansa: Aya ta farko tana nuni a kan yadda mutanen annabi Nuhu (a.s) suka roki a aiko musu da azaba. Aya ta biyu kuwa tana nuni a kan zuwan azaba da yadda suka halaka. Aya ta uku kuwa tana nuni ne a kan yadda Annabi Salihu (a.s) ya yi kira ga mutanensa bayan sun halaka, inda yake ce musu: Na isar da sakon Allah amma kun kasance ba ku son mai nasiha. Abin da kuwa yake nuni da cewa Annabi Salihu (a.s) ya yi magana da mutanensa bayan sun mutu abubuwa ne guda uku kamar haka: 1-Tsarin yadda ayoyin suka zo. 2-Harafin “fa†da ya zo a kalmar “fatawalla†wanda yake nuni a kan jeri, wato wannan kalma tana ba da ma’ana a kan kasantuwar abu daga wannan sai wannan wato bayan halakarsu, sai ya juya fuskarsa ya ce musu: 3- “Sai dai ku ba ku son mai nasihaâ€. Wannan yana nuna yadda suka yi nisa a wajen bijirewa Ubangiji, wanda bayan mutuwarsu ma suna da wannan siffa ta yadda ba su son mai fada musu gaskiya. Wannan aya tana nuna yana magana ne da ruhunan mutanensa, sannan ya nuna bayan mutuwarsu ma suna cikin wannan hali na suna rashin son nasiha. Tambaya: Maganar da annabi Salihu ya yi ba wai yana nufin da gaske yake ba, kawai yana magana ne kamar yadda mawaka sukan yi da bango ko kofa? Amsa: Idan mutum ya yi amfani da halin da yake a ciki yayin da ya yi wannan magana, sannan sai ya ce, ai Annabi Salihu ya yi magana ne kamar yadda mawaki yake magana da kofa da bango, to lallai mutum ya yi tafsiri ne kawai da ra’ayinsa, sannan wannan tafsiri bai inganta kuma kuskure ne a bayyane. Hakikanin tafsiri da ra’ayi shi ne mutum kafin ya fassara wata aya ya zamana yana da wata akida, saboda ya kare wannan akidar tasa sai ya yi tawilin zahirin aya ta yadda zata yi dai-dai da akidarsa, domin kuwa wanda yake da wannan ra’ayi saboda ba shi da imani da alakar da take akwai tsakanin wannan duniyar da rayuwar barzahu, babu makawa sai ya yi irin wannan tafsiri.
|