Rayuwa Bayan Mutuwa



Amma wadanda ba su yi imani da wani abu sai wanda kawai muke iya gani ko muke iya tabawa da makancinsu ba, Suna goyon bayan ra’ayi na farko ne wato hakikanin mutum bai wuce wannan jikin nasa ba. Ruhi a wurinsu bai wuce daidaitar gabobi ba, wato ruhi kawai sakamakon aiki da karbar aiki ne tsakanin gabobi, bayan wannan babu wani abu daban mai suna ruhi. Ruhi ya samu ne ta hanyar haduwar gabobi ta yadda mutum yake ji yake gani, saboda haka dukkan wannan babu wani abu daban wanda ba jiki ba. Haka nan sakamakon haduwar gabobi mutum yake ji yake gani, fushi da farin ciki, so da kiyayya da dai sauransu!

Saboda haka ruhi a wajen wadannan ba wani abu ne ba sai kawai abin da yake faruwa sakamakon haduwar jiki, ba wai wani abu ba ne wanda yake daban da jiki ba. Duk da cewa ma’abuta addini sun yi imani da cewa akwai wani abu mai suna ruhi wanda kuma yana da alaka da wannan jiki.

Bahasi a kan dalilan masu inkarin ruhi da dalilan suke kawowa da raddi a kan wannan tunani ba zamu iya kawo su ba a cikin wannan ‘yar karamar kasida ba[1], saboda haka a nan kawai zamu takaita ne da dalilan da malaman akida suke kawowa a kan hakan.

Malaman akida na muslunci suna bayyanar da hakikanin mutum ta cewa mutum bai takaita ba ga wannan jikin kawai, domin kuwa akwai wani abu bayan wannan kuma shi ne hakikanin dan Adam, kuma yana da wata alaka da wannan jikin, suna da bahasi mai fadi a kan haka sannan sun kawo dalilai guda goma da suke tabbatar da wannan da’awa ta su. Amma a nan zamu wadatu ne kawai da wasu daga cikinsu wadanda suka fi zama bayyanannu kuma kusan kowa zai iya gane su ya kuma yarda da su, sannan ana iya gwada su domin tabbatarwa.

1-Kalmar “Ni” wato “I” a cikin harshen turanci

Wannan kalma wacce kowa yake nuni da kansa da ita yayin da ya aikata wani abu, kamar ya ce; na ce, na tafi, na gani, na ci, na sha. Ba ma kawai ya takaita a nan ba, mutum yakan jingina dukkan gabobinsa zuwa ga wannan kalma yana cewa; kaina, zuciyata hannuna da dai sauransu…

Wani lokaci ma mutum yakan jingina dukkan jikinsa zuwa ga wannan kalma, yana cewa jikina, wannan al’amari na jingina ayyuka da gabobi da ma dukkan jiki ga wannan kalma ta “ni”to lallai zai zama ba jiki ba ne domin kuwa mutum ya jingina dukkan jikinsa zuwa gare shi wanda yake nuna wani abu ne daban.

Saboda haka a cikin kowane mutum akwai wannan hakika ta “ni” wacce kuma ita ba jiki ba ce. Wannan kuma shi ne hakikanin Mutum, Idan kuwa muka yi inkarin wannan abu wanda yake a fili, to dole ne ya zamana abubuwan da muka ambata a sama babu inda aka jingina su, tunda babu wannan hakika ta “ni”. Saboda haka tunda wannan hakika tana sama da jiki, don haka ita ba jiki ba ce wani abu ne daban wanda ba jiki ba. Duk da cewa yana da alaka da wannan jiki.

2-Kasantuwar mutum ba ya canzawa

Wata sheda ta biyu wacce take tabbatar da samuwar ruhi wanda yake daban da wannan jiki ita ce, Mutum tun daga farko rayuwarsa kowane lokaci cikin canzawa yake, amma akwai wata hakika wacce take ita ba ta canzawa a duk tsawon zamani.



back 1 2 3 4 5 6 7 next