Rayuwa Bayan MutuwaRayuwa Bayan Mutuwa Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id Sanin makomar mutum bayan mutuwa yana daya daga cikin abubuwan da mafi yawan mutane suke so su sani, sannan mafi yawa suna so su san hakikanin al’amarin mutuwa menene ita? Shin mutuwa shi ne karshen rayuwa, ta yadda fitilar rayuwar mutum zata dushe da zarar ya mutu, wato bayan mutuwa babu komai sai rashi? Ko kuwa mutuwa wata kofar shiga wata duniya ce wacce take tafi wannan duniyar daraja da haske, kuma hakikanin al’amari ma shi ne, mutum ya tsallake wata gada ce ta yadda ya fadacikin wata sabuwar rayuwa? A hakikanin gaskiya muna iya kasa batutuwan falsafa zuwa gida biyu kamar haka: 1-Batutuwan da suke masu zurfi wadanda kawai sai wadanda suka yi zurfi a cikin wannan fannin na falsafa, Su ne kawai zasu iya yin tunani har su bayar da ra’ayi dangane da hakan. 2-Batutuwan da suka shafi kowane mutum, ta yadda kowane mutum yana so ko yana tunani a kansu, wadannan kuwa sun hada da abin da ya shafi batun rayuwa bayan mutuwa.
|