Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)



 Sai Umar ya ce masa: Kana iya bi na mu tafi madina mu ziyarci kabarin Manzo ta yadda zamu fa’idantu da ziyararsa?

 Sai Ka’ab ya amsa wa khalifa abin da ya nema daga gareshi, ya yi shirin tafiya tare da khalifa. A lokacin da Umar ya shiga garin madina, farkon abin da ya fara yi shi ne ya shiga masallacin Manzo ne domin ya yi wa Manzo sallama.[3]

 Duk da yake ba mu da bukatar mu kafa sheda a nan da irin wadannan misalai, domin kuwa al’ummar musulmi duk tsawon karnoni sha hudu sun dauki wannan al’amari na ziyara Manzo a matsayin mustahabbi kuma suna tafiya Madina domin su aiwatar da wannan mustahabbi.

 Subki dangane da tafiyar ayari-ayari zuwa ziyarara Manzo ya yi maganganu da dama akan hakan, ya kara da cewa masu ziyara bayan sun gama aikin hajji suka kama hanyar Madina ne domin su kai wa Manzo ziyara, ya kara da cewa: wata sa’a sakamakon fahimtar ladar da yake cikin yin hakan sukan dauki hanyar da tafi nisa zuwa Madina, domin su samu lada mai yawa a kan haka. Sannan ya cigaba da cewa, wadanda suke tunanin cewa dalilin da ya sa mutane suke tafiya madina shi ne domin su ziyarci masallacin Manzo kuma su yi salla a ciki wannan kuskure ne, domin kuwa abin masu ziyarar suke fada ya saba wa wannan tunanin. Domin manufarsu a kan wannan ziyara shi ne su ziyarci kabari Manzo, sannan wannan shi ne gurinsu na ziyarar Madina.

 Domin kuwa idan manufarsu a kan wannan tafiya shi ne ziyartar masallaci me ya sa ba su tafiya Kods domin su ziyarci masallacin baitil mukaddas wanda yin salla a cikinsa bai gaza wa yin salla a masallacin Manzo ba?

 Kamar yadda yake haduwar malamai a kan wani hukunci yana nuna ingancin wannan hukunci a shari’a haka nan haduwar dukkan musulmi a kan wani aiki yana nuna mafi daukaka kasantuwan wannan abin a cikin shari’a.[4]

 

Masu Haramta Tafiya Don Ziyarar Manzo

 Har zuwa karshen karni na bakwai malamai sun hadu a kan wannan al’amari cewa tafiya domin aiwatar da wani aiki na mustahabbi koda ba ta zama mustahabbi ba to alal akalla ta halasta. Amma a farkon karni na takwas, Sai Ibn Taimiyya ya yi riko da hadisin Manzo wanda Abu Huraira ya ruwaito ta yadda ya saba wa dukkan malamai da suka hadu a kan wannan al’amari. Wannan ruwaya kuwa da Ibn taimiyya ya yi mafani da ita, an ruwaito ta ne ta fuska guda uku, amma abin da yake iya tabbatar wa Ibn taimiyya da manufarsa ya zo da fuska biyu ne kamar haka:

1-Kada a yi nufin tafiya sai zuwa masallatai guda uku: Wannan masallaci nawa, masallacin ka’aba da Masallacin Kods.[5]



back 1 2 3 4 5 6 7 next