Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w) Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id Ziyarar Kabarin dukkan musulmai da musamman ziyarar kabarin Manzo wani abu ne Wanda yake mustahabbi mai karfi a cikin musulunci. Sannan malaman hadisai daga Sunna da Shi’a sun ruwaito hadisai da dama a kan mustahabbancin ziyarar kabarin Manzo wadanda wasu daga cikinsu sun gabata a cikin bahasin da ya gabata ta yadda babu wani malami daga cikin malaman musuluncin da ya ba wa kansa damar yin shakku a kan mustahabbancin ziyarar Manzo. Wannan kuwa ya hada har da Muhammad Bn Abduh wanda yake da wasu masatlolin dangane da abin da ya shafi annabawa, a nan ba kawai ya yi shiru ba ne, sai dai ya yi magana a kan mustahabbcin ziyarar Manzo (s.a.w). Sannan mun kawo abin da yake cewa dangane da hakan a bahasimmu na baya. Tare da la’akari da kasantuwar mustahabbicn ziyarar Manzo, amma msulmi sun kasu akan wannan kyauata ta Ubangiji: 1-Mazauna Madina Mazauna Madina sakamakon makwabtaka da suke da ita da Manzo (s.a.w). Suna iya ziyartarsa ba tare wata wahala ba don aiwatara da wannan mustahabbi. 1-Mazauna sauran wurare a cikin duniya
|