Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma



 Kai har da babban mai fatawar Kasar Sa’udiyya wato sheikh Abdul Aziz Bn Baz ya ba da fatwa a kan mustahabancin ziyarar kabarin Manzo mai girma.[3]

 Kawo dukkan maganganun malamai a kan wannan al’amari, ba zai yiwu ba a wannan wuri, saboda haka kawai zamu wadatu da kawo wasu daga ciki ne kawai kamar haka:

1-Abu Abdullaji Jujani Shafi’i (ya rasu a shekara ta 403) Bayan ya yi maganganu a kan girmama Manzo sai yake cewa: A matsayin tuanatarwa a yau ziyarar Manzo shi ne ziyarar kabarinsa mai albarka.[4]

2-Abu Hasan mawardi (ya rasu a shekara ta 450) Yana rubuta cewa: Jaogoran matafiya zuwa aikin hajji bayan an gama aikin hajji sai ya jagoranci twagarsa zuwa madina domin mahajjata su hada ziyara guda biyu, wato ziyarar dakin ka’aba da ziyarar kabarin Manzo. Ta haka ne zasu kiyaye martabar Manzo suka kuma bayar da hakkinsa na biyayya gare shi. Ziyarar kabarin Manzo ba ya daga cikin farillan ayyukan hajji, amma yana daga cikin mustahabban aikin hajji.[5]

3-Gazali ya yi bayani mai fadi dangane da ziyar Manzo (s.a.w). Sannan ya yi bayani a kan ladubban ziyarar Manzo Yana cewa: Manzo ya ce: ziyarata yayin da ba ni da rai duk daya ne da ziyarata a lokacin da nake raye. Sannan duk wanda yake da karfin jiki da dukiya amma bai ziyarce ni ba to ya yi mani tozarci.

 Gazali yana karawa da cewa: Duk wanda ya yi nufin ziyarar Manzo to ya aika masa da gaisuwa a bisa hanya, sannan a lokacin da idonsa ya hangi itatuwa da bangayenmadina sai ya ce: Ya Allah wannan shi ne haramin Manzonka ka sanya shi kariya a gareni daga wuta, Sannan ya zama aminci a gare ni daga azabar wuta da munin hisabi.

 Sannan gazali ya yi tunatarwa dangane da ladubban ziyarar Manzo yana rubuta cewa: Wanda ya ziyar Manzo sai wuce a “Bakiyya”don ya ziyarci kabarin Imam Hasan Bn Ali (a.s) Sannan ya yi salla a masallacin Fadima (a.s).[6]

4-Alkali Iyadh maliki (ya rasu a shekara ta 544) yana rubuta cewa: Ziyara Manzo wata Sunna ce wadda kowa ya aminta da ita.

 Sannan ya ruwaito wasu hadisai dangane da ziyarar kabarin Manzo sannan yana karawa da cewa: maziyarcin kabarin Manzo, to ya kamata ya nemi tabaraki da wurin ibadar Manzo (Raudha) Minbarinsa, wurin da yake tsayawa, da shika-shikan da Manzo yake jingina a wurinsu da kuma wurin da jibra’il yake saukar wa Manzo da wahayi. [7]

5-Ibn Hajjaj Muhammad Bn Abdali Kirawani Maliki (ya rasu a shekara ta 738) bayan ya yi Magana dangane da ziyarar manzanni da ladubbanta da yadda ake yin kamun kafa (tawassuli) da su da neman biyan bukata daga garesu, sai ya tunatar dangane da ziyarar kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next