Sakon Ali a.s ga Malik Ashtar
Siyasar jagora ga masu zuwa don bukatunsu Ka sanya wa masu bukatau wani lokaci da zaka ba su (ka hadu da su) da kanka, ka zauna da su zaman shekara sai ka kaskantar da kai a cikinsa ga Allah da ya halicce ka, kuma ka zaunar da rundunarka da mataimakanka daga masu tsaronka da 'yan sandanka don mai yin magana daga cikinsu ya yi maka magana ba tare da wani tsoro ba, hakika ni a wurare da yawa na ji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Al'umma ba zata tsarkaka ba matukar ba a karbar wa mai rauni hakkinsa daga mai karfi, ba tare da wani tsoro ba". Sannan (su wadannan raunanan al'ummarka da ka zauna da su) sai ka jure wa kaushin maganarsu, da kasa maganarsu (a gabanka), ka kawar musu da kuncin ransu, da girman kai, to (idan ka yi haka), Allah zai shimfida maka lullubin rahamarsa, ya wajabta maka samun ladan biyayyarsa. Kuma ka bayar da abin da ka bayar kana mai saukakawa, (idan kuwa babu to sai) ka hana a cikin (fadin) kyakkyawar magana, da kawo hanzari.
Tsarin kowace rana na jagora Akwai wasu abubuwan da babu makawa kai zaka yi su da kanka: Daga ciki amsa wa ma'aikatanka abin da sakatarorinka ba zasu iya ba. Biyan bukatun mutane yayin da aka kawo su, na daga abin da mataimakanka suke jin haushin yin sa (sau da yawa wasu mataimakan ba sa son biyan bukatun mutane da wuri don girman kai ko don wani amfani nasu). Kuma ka zartarwa kowace rana aikinta, ka sani kowace rana tana da ayyukanta, ka sanya mafi kyawun lokuta tsakaninka da Allah (s.w.t), ka girmama wannan bangarorin, duk da yake dukkaninsu (lokutan Allah da na mutanen) na Allah ne idan niyya ta kyautatu a cikinsu, al'umma ta samu salama daga garesu. Ya kasance daga cikin kebantaccen abin da kake bayar da shi ga Allah kawai na addininka shi ne tsayar da wajiban da suke nasa ne kawai. To ka ba wa Allah wani abu na jikinka da darenka da ranarka, ka cika (kyautata) abin da kake kusanta da shi zuwa ga Allah daga wadannan (ibadojin) cikawa ba tare da ragewa ko tauyewa ba, ko me kuwa zai yi wa jikinka. Kuma idan ka tsayu don yin salla da mutane kada ka zama mai korewa (mai sanya wa mutane kyamar jam'i saboda dadewa da jan doguwar raka'a) ko mai tozartawa (mai tauye wasu rukunoni na salla), ka sani a cikin mutane akwai wanda yake da matsala (kamar rauni don tsufa ko yarinta ko rashin lafiya) da mai bukata (da yake son ya gama salla da wuri). Hakika na tambayi manzon Allah (s.a.w) yayin da ya tura ni zuwa kasar Yaman cewa yaya zan yi salla da su, sai ya ce: Yi salla da su kamar sallar mafi raunin cikinsu, ka kasance mai tausayi ga muminai.
Cutarwar jagora ya kange kansa daga mutane (Ganawar jagora kai tsaye da mutane) Kuma bayan haka kada ka tsawaita kangiyar kanka daga mutane, ka sani kangiyar jangorori daga al'umma wani abu ne na (mai kawo) kunci, da karancin ilimi a lamurran (kasa). Kuma kange su yana yanke musu sanin abin da aka kange musu shi, sai abu mai girma ya zama karami gunsu, karamin abu kuma ya girmama gunsu, kyakkyawa ya munana (gunsu), mummuna ya kyautata (gunsu), gaskiya kuma ta cakude da karya. Ka sani shugaba mutum ne da bai san abin da mutane suke boye masa shi ba na lamurra, kuma babu wata alama a kan gaskiya da ake gane nau'o'in gaskiya da karya da ita. Kai dai daya daga cikin mutane biyu ne: Ko dai mutum ne wanda ranka take da baiwar kyauta bisa gaskiya, to a kan me zaka kange mutane daga samun wajibin hakkin da kake bayarwa ko wani kyakkyawan karimci da zaka yi shi. Ko kuma dai kai (mutum) ne da aka jarraba da yin rowa, to ai nan da nan ne mutane zasu daina tambayarka idan suka yanke kauna daga samun kyautarka, tare da cewa mafi yawan bukatun mutane wurinka babu wani abu mai nauyi a kanka cikinsu, (su bukatun sun hada da) wata kara ce kan wani zalunci, ko neman yin wani adalci a wata mu'amala. Sannan ka sani shugaba yana da wasu kebantattun mutane abokan shawara na musamman da suke da son handuma da babakere (a kan komai), da karancin adalci a mu'amala, to ka yanke tushen (wannan hali) nasu da yanke dukkan sabuban wadannan munanan halaye (nasu).
Hadarin kebance wani Daji ko fili ga na gefensa Shugaba (Siyasar jagora tare da makusantansa da na gefensa) Kada ka kebance wa wani daga na gefenka da makusantanka da wani babban daji, kada ya yi kwadayin samun wani babban yanki daga gareka da abin da zai zama cutarwa ga wanda yake makotaka da ita na daga mutane na wurin shan ruwa, ko wani aikin tarayya da zasu rika dora nauyinsa kan wasunsu, sai ya zamanto nasu shi ne jin dadin wannan (lamarin) ban da kai, kai kuma aibinsa yana kanka a duniya da lahira. Ka lizimci gaskiya (bayar da lada ko ladabtarwa) ga wanda ya lizimce ta makusanci ne ko manesanci, kuma ka kasance mai juriya mai neman lada a kan (zartar da) hakan, wannnan kuwa ya kasance ne daga 'yan'uwanka da kebantattun mutanenka ne ta yadda ya faru. Ka ladabtar da shi da abin da yake yi maka nauyi gunsa, domin sakamakon wannan yana da kyau. Idan kuwa al'umma ta yi maka zargin zalunci to ka yi musu bayani a fili da uzurinka, ka kawar da zatonsu a kanka da bayyanawarka, domin a cikin wannan abin (da zaka yi) akwai tarbiyyantar da kanka, da tausasawa ga al'ummarka, da bayar da uzuri da zaka iya isa zuwa ga bukatarka na daidaita su kan gaskiya.
Fifita siyasar yin sulhi a kan ta yin yaki (Siyasar zaman lafiya da kashedin yin gaba da kiyaye dukkan yarjejeniyoyi) Kada ka sake ka ki wani sulhu da wani makiyi ya kira ka zuwa gareshi don akwai yardar Allah cikinsa, ka sani a cikin sulhu akwai hutu ga rundunarka, da hutawa daga bakin cikinka, da aminci ga kasa. Sai dai ka yi hattara matukar hattara daga makiyinka bayan yin sulhu, domin tayiwu makiyi ya kusa da ya shammace ka ne, to ka yi riko da shiri, ka tuhumi kyautata zato a cikin (irin) wannan. Idan ka kulla wani alkawari da kai da makiyinka, ko ka sanya masa wani alkawari daga gareka, to ka kiyeye alkawarinka da cikawa, ka yi tsantsenin alkawarinka da kiyaye amana, ka sanya kanka garkuwa ga abin da aka ba ka (na alkawari), ka sani babu wani abu na wajibcin hukuncin Allah da mutane suka fi tsananin haduwa a kansa duk da (kuwa) rarrabuwar (kawukansu sakamakon) son ransu da (kuma) daidaitar (bambancin) ra'ayoyinsu, fiye da girmama cika alkawuran (yarjejeniyoyi). Kuma hakika wannan ya lizimci mushrikai a tsakaninsu banda musulmi yayin da suka samu bala'in sakamakon yaudara (a lokacin annabi). Don haka kada ka yi yaudarar alkawarinka, kada ka karya yarjejeniyarka, kada ka shammaci makiyinka, ka sani ba mai yi wa Allah karan tsaye (shisshigi) sai jahili tababbe. Kuma lallai Allah ya sanya alkawarinsa da yarjejeniyarsa aminci ne da ya bayar da shi ga bayinsa da rahamarsa, kuma hurumi ne da suke nutsuwa da shi zuwa ga kariyarsa, suke kwarara zuwa ga kariyarsa. Don haka babu barna, babu algush, babu yaudara a cikinsa.
Wajibcin bayani dalla-dalla a nassoshin yarjejeniyoyi Kada ka kulla wani abu da kake halatta yin jirwayen magana a cikinsa, kada ka dogara kan jirkita magana bayan karfafawa da kullawa, kada kuncin lamarin da (daukar alkawarin yarjejeniyar) ya lizimta maka (na daga) alkawarin Allah a cikinsa ya nemi ka bata shi ba tare da wani hakki ba, ka sani hakurinka kan kuncin wani lamari da kake sauraron mafitarsa da samun kyakkyawar mafitarsa shi ya fiye maka yin yaudara da kake jin tsoron mummunan sakamakonta, kuma (idan ka yi yaudara ka karya yarjejeniyar) wani mummunan (zunubi) ya kewaye ka daga Allah wanda ba zaka iya samun mafita a cikinsa a duniyarka ko a lahirarka ba.
Kashedin siyasar kisa da zubar da jini (Kashedi mai tsanani ga jagora daga zubar da jini) Kuma na hana ka zubar da jini ba tare da halal dinta ba, domin babu wani abu da ya fi kawo azaba, wanda yake mafi girma ga mummunan sakamako, kuma mafi kusa da gushewar ni'ima da yanke rayuwa, fiye da zubar da jini ba tare da hakki ba. Kuma Allah madaukaki zai fara hukunci tsakanin bayi ne cikin abin da suka zubar na jini ranar kiyama. Don haka kada ka karfafi mulkinka da zubar da jinin haram, domin wannan yana raunana shi ya rusa shi, kai yana kawar da shi ne ya ciratar da shi. Kuma ba ka da wani uzuri wurin Allah ko a wurina a kisan ganganci, domin akwai sakamakon kisasi a cikinsa. Idan kuwa aka jarrabe ka da (kawo maka wani mutum wanda ya yi kisa bisa) kuskure, (sai ka zartar da) hukuncinka (a kansa amma sai ka samu bisa kuskure hukuncin da ka zartar) ya samu wuce iyaka da bulalarka ko takobinka ko hannunka da wata ukuba (bisa kuskure, kamar a wurin kisasin wata gaba sai aka wuce iyaka), to ka sani a cikin (kowane kuskuren zartar da hukunci ko da kuwa) naushi (ne) da abin da ya yi sama da hakan (kamar ya kai ga kashe shi, to) akwai (yiwuwar) kisa, don haka kada tumben (takamar) mulkinka ya sanya ka daga kai har ka hana ma'abota jini hakkinsu (na kisasi ko diyya).
Kashedin son jagora ga yabo da kambamawa Ka yi hattara da jin kanka da amintuwa da abin da yake burge ka daga kanka, da son yabo (gareka), domin wannan ita ce mafi samun damar shedan, domin ya shafe maka abin da kake (da shi) na kyautatawar masu kyautatawa.
Maganar daula mai tawali'u ga 'yan kasa (Dokokin siyasar jagora tare da mutanen kasa) Na hana ka yi wa al'ummarka gorin kyautatawarka, ko neman su kambama abin da ka yi na aikinka, ko ka yi musu alkawari sai ka bi alkawarinka da sabawarka, ka sani yin gori yana bata kyautatawa ne, neman kambamawa yana tafiyar da hasken gaskiya, saba alkawari yana jawo kiyayya gun Allah da gun mutane. Allah madaukaki yana cewa: "Zargi (zunubi) ya girmama gun Allah ku fadi abin da ba kwa aikatawa".
Daidaito a mu'amalar shugaba cikin al'amura (Tabbata da daidaito a wurin daukar matakai) Kuma na hana ka yin gaggawa a lamurra kafin lokacinsu, ko kuma ka saryar da su (ka fasa yin su bayan an zartar da) yayin da za a yi su, ko kuma yin taurin kai a cikinsu idan aka yi su, ko raunana su idan suka bayyana, ka sanya komai a mahallinsa, ka ajiye kowane aiki a wurinsa.
Hana shugaba kebance kansa da damarmaki da abubuwa Kuma na hana ka kebance (kanka) da abin da yake mutane suna da daidaito a cikinsa, da yin banza da abin da ake nufi da shi (na hadafinsa) na daga abin da ya bayyana ga idanuwan (mutane), ka sani shi (abin da ka wawashe na al'umma) abin karba ne (don a mayar da shi) ga waninka (na al'umma masu hakki a lahira) daga gareka (domin saka wa al'umma), kuma da sannu ba dadewa (a lahira) abubuwan da suka boyu (a nan duniya) zasu bayyana (a lahira), a yi wa wanda ka zalunta (na daga al'umma) adalci kanka.
Matsayin shugaba yayin fushi (Yaya shugaba zai kasance mai iya hade fushinsa) Ka mallaki shisshigin kanka, da zafin ranka, da tsananin hannunka, da kaifin harshenka, ka kiyaye dukkan wannan da kame yin munanan maganganu, da jinkirta hukunci har sai ka sauka daga fushinka (tukun) ka samu (hucewa daga haushinka da samun) zabi (sannan sai ka zartar da hukunci). Kuma ba zaka iya hukunta wannan a kanka ba har sai ka yawaita bakin cikinka da tuna makoma zuwa ga ubangijinka, kuma wajibi ne ka tuna abin da ya gabata na wadanda suka gabace ka daga hukumomin adalci, ko wata al'ada mai kyau, ko wani aiki (da aka samo) daga annabinmu, ko wata farilla a littafin Allah, sai ka yi koyi da abin da ka gani daga abin da muka yi aiki da shi a cikinsa, ka yi matukar kokarin kanka na ganin ka yi biyayya ga wannan rubutu nawa da na aiko maka da shi wanda na amintu da shi na daga hujjojin kaina gareka don kada ka samu wata matsala yayin gaggautawar kanka zuwa ga son ranta.
Addu'ar Imam Ali gareshi da dacewa wurin tabbatar da hadafinsa a hukuma Kuma ni ina rokon Allah da yalwar rahamarsa da girman kudurarsa kan bayar da dukkan abin nema, da ya ba ni dacewa da ni da kai bisa abin da yake akwai yardarsa cikinsa na tsayuwa kan uzuri bayyananne zuwa gareshi da halittarsa, tare da kyautata yabo cikin ibada, da kyakkyawan tasiri cikin gari (kasa), da cikar ni'ima, da ninka karimci, kuma ya cika mana ni da kai da rabauta da shahada, kuma mu masu kwadayi ne zuwa gareshi. Kuma aminci ya tabbata ga manzon Allah (s.a.w) da alayensa tsarkaka (a.s)
Godiya ta tabbata ga ubangijin talikai
|