Kabilancin Shi'anci



Kuma a fili yake ke nan cewa ambaton Salim yana nuna mana cewa halifa bai shardanta Larabci ba, in ba haka ba, da ya yi nassi a kan Larabci kawai, kuma manyan mu’utazilawa sun tafi a kan hakan kamar Diraru dan Amru, da Sumama dan Asrash da Jahiz, da yawa daga wasunsu.

Kamar yadda Hawarijawa dukkaninsu suka tafi a kan rashin sharadin larabcin halifa da nassinsu karara kan hakan. Kuma a bisa wannan rashin sharadin nan Hanifawa suka tafi, kuma saboda haka ne ma suka inganta halifanci Daular Usmaniyya. Wannan sharadin na kasancewar halifa balarabe a bisa hakika ba yadda za a yi ya kasance sakamakon kabilanci domin wannan ba zai yiwu ba a sakon addinin musulunci wanda yake sakon karshe kuma addinin daidaito, sai dai da wannan sharadin musulunci yana iya kiyaye mana samuwar shugaba wanda ya san zurfin abin da shari’a ta kunsa da kuma wayewar da take da alaka da harshen Larabci, don haka musulunci yana iya sanya sharadin Larabci ga jagora ba tare da kuma ya tauye wasu ba ko kuma ya muzanta matsayinsu ko kuma ya soki ikhlasinsu ba.

4- Tarihi da Maslaha

Tarihin Shi'a da muka kawo wani bangare ne na tarihin jazirar Larabawa da dukkan abin da ya shafe ta wanda ya danganci tarihi. Haka nan ma maslahar da aka yi tarayya a ciki da kuma tsarin tunani da al’adu na al’ummar. Don haka ne ma sai musulunci ya yi kokarin ganin ya tseratar da musulmi daga dukkan wani abu da zai kawar musu da al’adunsa abin da yake wani abu ne da shi ne ya hada dukkan mazauna jazirar Larabawa. Kuma wannnan abu ne abu bayyananne da ba ya bukatar tsawaita bayani kansa, don haka ne ma zamu wadatu da abin da muka ambata, kuma dai da wannan bayanin da muka kawo ne zai bayyana a fili cewa Shi’anci a hakikaninsa balarabe ne tun farko, kuma a nan ne aka rene shi, don haka ne marubuta suka tafi a kan cewa Shi’anci balarabe ne gaba dayansa, wato; ina nufin marubuta na wannan lokacin domin kuwa wannan mas’ala ce da a zamanin farko ba ta cikin tunanin Shi'a na wancan lokacin na farko, batun raba wa Shi’anci asalin Farisanci ya faru ne daga karshe bayan Farisawa sun zama Shi'a tun daga karni na goma, amma tarihin lokacin da ya gabaci karni na goma babu wasu Farisawa da suke Shi'a ne sai ‘yan kadan, kuma da sannu zamu yi magana game da hakan dalla-dalla. To lokacin da Farisawa suka zama Shi'a to a wannan lokacin ne sai ga shi ana bayyanar da aibobinsu da lokacin da suke sunnanci ba a fade su ba, kuma in Allah ya yarda zamu fitar da natijar haka a bahasosi na gaba.

Yanzu bari in kawo maka wasu misalai daga bayanin da wasu marubuta suka kawo game da wannan mas’ala da musun larabcin Shi’anci a lokacin da suke son zagin Shi’anci ta hanyar zagin Farisawa da kuma bayanin munanan halayensu sai ka saurara ka ji me suke cewa:

1- Dakta Ahmad Amin:

Ahmad Amin yana fada a cikin abin da muka kawo a baya kuma muka ambaci wani abu da ya shafi maganar da muke kai yana mai cewa: Abin da tarihi ya kawo masa shi ne; Shi’anci ya fara kafin shigar Farisawa cikin musulunci ne amma sai dai wannan da ma’anarsa mai sauki da take nufin Ali (a.s) ya fi waninsa cancanta ta fuska biyu; ta fuskacin kimarsa da kusancinsa da Annabi (s.a.w). Sai dai wannan Shi’anci ya samu wani yanayin salo daban ta hanyar shigar da wasu fikirori da akidu a cikinsa (a musulunci) na yahudanci da kiristanci da majusanci, kuma tun da dai wanda suka fi kowa shiga musulunci su ne Farisawa to suna da tasiri mafi girma a Shi’anci. Ra’ayinsa a nan a fili yake cewa shi’an farko ba Farisawa ba ne, duk da ya warware maganarsa a wani wurin.

2 Dakta Ali Husain Kharbudali ya ce:

Akwai wasu jama’a na Larabawa da suke biyayya ga Ali bayan halifanci ya koma hannun Abubakar, kuma Jolad Tasiher yana cewa: Wannan harka ta Shi’anci ta faro ne daga kasashen Larabawa tsantsa kuma sai da yawa daga kabilun Larabawa suka fantsama da wannan ra’ayoyin na jagorancin hukumar Allah, da shar’anta hakkin Ali (a.s) kan halifanci, sai mutanen Farisa a Iraki suka yi riko da koyarwarsu da dukkan kumaji, suka ga cewa Imamanci ba wani abu ne da ake ba wa al’umma hakkin ayyana jagoranta na musulmi da kanta ba ne, sai dai shi wani abu ne na jagorancin addini da jagorancin musulunci, don haka ya wajaba Allah ya ayyana Imami jagora kuma ya kasance ma’asumi, kuma Ali (a.s) shi ne wanda Annabi (s.a.w) ya ayyana shi.



back 1 2 3 4 next