Kabilancin Shi'anciFasali Na Uku Hakikanin Kabilancin Shi’anci da Ra’ayoyin Marubuta a Ciki A farkon wannan bahasi mun kawo tambaya kan ma’anar Larabci da abin da yake zuwa a kwakwalwa a matakin farko na cewa balarabe shi ne wanda ake haifa da iyaye biyu Larabawa, kuma wanda ya gangaro daga jinin Larabci, sai dai wannan wani abu ne da ba zai yiwu ba domin ba zamu iya samu jini dari bisa dari ba wanda bai samu wata cakuda ba, kuma domin cewa jinin mutane dukkaninsu yana komwa zuwa ga madogara kuma asali daya ne duk ya cakuda, don haka sai mu nemi wata ma’ana daban, sannan kuma ba yadda zamu sawwala cewa jini yana tasirantuwa ne da akida da tunani da al’adu, me ke nan abin nufi da Larabci a wannan lamarin, sannan kuma duk da haka wannan ra’ayi yana iya tsayuwa a kan kaddara samuwar jini na Larabci tsantsa wanda yake tunani ne ba na ilimi ba, kuma ba zai yiwu a dogara da shi ba. Idan ma mun sassauta mun yarda da ingancin wannan maganar, mun riga mun ambaci cewa 'yan Shi'ar da Shi’anci ya fara da su duk sun kasance daga kabilun Larabawa ne, kuma mun kawo dabaka ta fari daga cikinsu, don haka ba ma ganin mu dora wahala ga mai karatu kan wannan, don haka sai muka kawo masa dabaka ta biyu da ta uku, kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga manyan littattafan da suka yi bayani game da mazajen domin ya ga mafi yawansu daga Larabawa ne. Sannan kuma idan mun kaddara cewa akwai wani jini tsarkakke da bai tasirantu da waninsa ba, to wannan maganar kawai ce, muna iya komawa maganarmu ta farko don mu ga mene ne ma’anar Larabci, zamu ga amsa ita ce; Larabci (a kabilance) ya hadu ne da tunani da al’adu da lugga (yare da harshe) da kuma kasa, don haka fahimtar ma’anar kabilar Larabci daga wadannan abubuwan ita ce fahimta mai inganci sahihiya, kuma ita ce take iya iyakance mana hakikaninsa, kuma mafi yawan rubuce-rubuce da suka iyakance hakikanin mutum sun karfafi wannan dalilai, wato; yare da tarihi da yanayi da kuma maslahar da aka yi tarayya a ciki sukan hadu su samar da abin da zai iya sanya a dangantu zuwa ga wata al’umma, don haka ne muna iya kawo magana game da Shi’anci ta fuskanci wadannan abubuwan sai mu fara da dalili na farko kamar haka: Abubuwan da suke hada hakikanin jini (kabila) 1- Yanayin Kasa: Yankin Larabawa shi ne wurin da aka reni Shi’anci tun farko, domin shi’ar Ali (a.s) na farko sahabbai ne kuma daga jazirar Larabawa kamar yadda muka kawo a baya, kuma idan an samu mutum daya ko mutane biyu kamar Salman Farisi da Abu Rafi’i Al’kibdi to muna iya ganin rayuwarsu a tsawon lokacin rayuwarsu a Hijaz ne, kuma daga Hizaj ne Shi’anci ya yadu zuwa sasannin kasa kamar Iraki da Siriya da Misira da Sham, da Afrika, da Indiya, da Khalij, da Turai, da Amurka, da Kasar Sin, da Rasha, da wasunsu na daga sasannin duniya tsawon shekaru masu yawa. Sannan kuma zamu ga maganar masu rubutu a kan wannan da kuma bayaninsu na cewa jazirar Larabawa ita ce wurin da aka haifi Shi’anci na farko. 2- Lugga (harshe) Ana ganin harshe shi ne babban dalilin da yake sanya kirga mutum cikin wata kabila, domin yare wani yanki ne na al’ada, kai binciken karshe ya tafi a kan cewa shi yanki mai girma na tunani mai magana. Wannan kuwa saboda sun kasa tunani kashi biyu ne, akwai; tunani mai shiru da kuma mai magana.
|