Shi’anci Lokacin Annabi Daga abin mamaki sai ga shi Alusi a cikin tafsirinsa na Ruhul Ma'ani ya tsaya a kan wata matsaya da take mai muni da rauni yana mai hana saukar wannan aya game da Ali (a.s), yana kuma fadawa cikin ta’assubanci da yakan kai mutun ga fadawa cikin kiyayya da gaba da gaskiya, da fadawa cikin magana mai karo da juna da warwara maras ma’ana. Mutum yakan yi mamakin wannnan mutumin, domin sau da yawa mukan gan shi da matsayin warware magana da suka ga Imam Ali (a.s), wani lokaci ya ba shi hakkinsa, wani lokacin kuma ya tsaya yana mai musun sa, kuma dukkan wanda ya karanta rubuce-rubucen Alusi ya san shi da hakan. C- Mataki na uku: Matakin da Annabi (s.a.w) ya dauka ranar Gadir Khum, yayin da ayar nan ta sauka: "Ya kai wannan Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka, idan kuwa ba ka aikata ba, to ba ka isar da sakonsa ba, kuma Allah ne yake kare ka daga mutane" Ma’ida: 69. Yayin nan sai Annabi (s.a.w) ya tsayar da matafiya kuma aka yi masa mimbari daga kayan rakuma sai ya yi huduba a kansa da hudubar nan tasa mashahuriya sananniya sannan sai ya rike hannun Imam Ali (a.s) ya ce: Ba ni ne na fi cancantar jagorantar muminai ba fiye da kawukansu? Suka ce: Haka ne. Sai ya maimaita sau uku, sannan sai ya ce: "Duk wanda nake jagoransa to Ali wannan jagoransa ne, Ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi, ka ki wanda ya ki shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka kuma tabar da wanda ya tabar da shi" sai halifa na biyu ya hadu da shi ya ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya kai dan Abu Dalib, ka zama shugabana kuma shugaban dukkan wani mumini da mumina. Kuma Razi ya kawo fuskoki goma daga cikin sababin saukar wannan aya; kuma daga cikin akwai cewa ta sauka Ibn Hamza Alhanafi ya kawo shi daga Abiddufail Amir dan Wa’ila kamar haka ya ce: Usama dan Zaid ya ce da Ali: Kai ba jagorana ba ne, kawai jagorana shi ne manzon Allah (s.a.w), sai Annabi (s.a.w) ya ce: Kamar dai ni an kusa kira na sai in amsa, kuma hakika ni zan bar muku nauyaya biyu, daya ya fi daya girma, littafin Allah da kuma Ahlin gidana, ku duba yadda zaku maye mini a cikinsu, ku sani ba zasu rabu da ni ba, har sai sun riske ni a tafki, kuma Allah shi ne shugabana, kuma ni ne shugaban dukkan mumini da mumina, kuma duk wanda na kasance shugabansa, to Ali (a.s) shugabansa ne, ya Ubangiji ka agaza wa wanda ya bi shi, kuma ka ki wanda ya ki shi[5]. An wallafa littattafai masu yawa daga bangaren Sunna da Shi'a littattafai kusan guda ishirin da shida[6] kan al’amarin Gadir, ba kuma ina son magana game da hadisin Gadir ba ne a nan game da jagorancin Imam Ali (a.s) da kuma shugabantar da shi a kan dukkan sahabbai, domin wannan al’amari ne da aka yi bincike masu yawa kansa ta fuskancin masu bincike, sai dai ni a nan ina son tambayar Dakta Ahmad Shalbi ne wanda yake cewa hadisin Gadir bai zo ba sai a littattafan Shi'a, ina mai tambayarsa shin akwai jin wani abu mai nauyi a kansa da ya dame shi ne da yake jin takaicin mas'alar Gadir da ayyana Imam Ali (a.s) a matsayin halifan annabi kuma jagoran musulmi, shi da ire-irensa na daga wadanda suke jifa da magana a kan iska, ka sani abin da yake kanka wanda ka sani na ilimi kana dauke da amana ne ga jama’a mai zuwa, kuma daga cikin kiyaye wannan amana shi ne ka gaya musu cewa irin littattafanka na Sunnanci sun zo da wannan magana daga madogararsu. Idan ka kasance kuma ba ka karatu ne, ko kuma kana karatu amma ba ka son ka sani to abin da ya fi maka shi ne kai shiru sai Allah ya ragwanta maka fiye da ka yi wannan al’amari bisa jahilci ko kuma bisa ta’assubanci. Kuma haka nan wanda yake cewa: Maula a wannan hadisi tana nufin dan ammi shi ma kamar Dakta Shalbi yake, domin dogaro da cewa tana daga cikin ma’anoninta, kuma ni ba zan tsaya yi wa wannan raddi ba, sai dai ina cewa ne: Allah ka kiyaye mana hankulanmu daga shafewa. wannan ba komai ba ne sai daya daga misalan wuraren da Annabi ya yi nuni da falalar Imam Ali (a.s) kuma wadannan wurare suna da yawa ba tare da sun karfafa mutane a kan Ali (a.s) ba, kuma ba tare da sun tura su ga sanin cewa shi ne wasiyyin Annabi ba, wanda yake Kur'ani ya sanya shi daya daga cikin masu shugabanci na gaba daya bayan Allah da manzonsa. Sannan kuwa ba makawa ne musulmi su yi biyayya ga abin da ya zo musu na ma’anar Shi’anci da muke fada cewa Annabi (s.a.w) ne farkon wanda ya dasa shukarsa, kuma ya girmama ya yadu tun a lokacin rayuwarsa, ya yi â€کya’ya, har ma da wasu mutane da aka san su da shi’ar Ali, wadanda suke a gefensa, suna masu nuni da shiryarwa a kan hakan, kuma da sannu zamu kawo sunayen na farko daga cikin sahabban da aka san su da Shi’anci da biyayya da mika jagoranci ga Ali (a.s). Daga Littafin Sheikh Wa'ili Na HAKIKANIN SHI'ANCI Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id [1] Alfirak wal makalat na nubkhati: Babin ta’arifin Shi'a. [2] Tarihin Dabari; j2, shafi: 216. da tarihin bin asir, j 2, shafi: 28. [3] Tafsirin Arrazi, j 3, sahfi: 431. [4] Assawa’ikul muhrika, babi na biyu daga fasali na [5] Albayan watta’arif, j 2, shafi 136. [6] A’ayanusshi’a, j 3, babul Gadir.
|