Zuciya da TunaniHankali: ana amfani da shi da ma'anar tunani wani lokaci, ko zuciya, ko da ma'anar da ilimin Falsafa (Philosophy) yake bincike. Kan abubuwa fasu fadi gama-gari Unibersal, kuma yana daukar ma'anar binciken da Mantik (logic) da Lissafi (mathematics) suke bincike kansa. Hankali shi ne jagora gaba daya a samuwa wanda yake saman komai, kuma shi ne ake kira da sunaye mabambanta idan an yi la'akari da shi ta fuskoki daban-daban, sai dai babban kashinsa shi ne: 1.Riskar ayyukan mutum, ta fuskacin jagoranci kan aikata su, da kuma 2.Riskar warwara (analysis) kan abubuwan da yake fuskanta na ilimi. Duk wadannan bangarori biyu masu muhimmanci suna koma wa gareshi ne. kuma ana kiran kowanne da HANKALI. Idan aka rasa na farko sai a rasa halaye na gari, sai mutum ya kasance shedani a cikin al'umma, sai ayyukansa su muzanta su munana ta yadda kowa yana kyamarsa, domin yana iya zama tantirin fasiki, ko mujrimin mutum. Don haka ne ma mai biyayya ga Allah sai a ce yana da HANKALI domin ya yi amfani da hankalinsa wurin tsarkake ransa. Idan kuwa aka rasa shi hankali a bangare na biyu; sai mutum ya rasa ilimi, ya kasance jahili, kowace guguwa tana iya kwasarsa domin ba shi da ilimi, kuma sai ya yawaita bin camfe-camfe, da jita-jita, da akidoji marasa tushe, shi wannan halakarsa a kusa take, sai ya halaka a akida, da tunani, da sauransu. Don haka ne ake ganin masu ilimin sanin Allah ko Hikima (Falsafa) da sauran ilimomi da cewa su ne masu HANKALI da wannan ma'anar. Tunani yana nufin wadannan surorin da suke taruwa a kwakwalwa kuma ake sawwala su a cikinta, suna iya kasancewa daidaiku, kamar ma'anar mutum wacce daidaikun mutane suke siffantuwa da shi. Kuma tana iya kasancewa jimla ce kamar fadinmu cewa: Allah daya ne! kuma duk wata tattaunawa da ake yi har a kai ga samun natijarta, duk dan Adam yana amfani da wadannan surorin da suke cikin kwakwalwarsa ne, ya harhada su, sannan ya cimma sakamakon da yake son kaiwa gareshi. Wadannan surorin duka da suke cikin kwakwalwa ana kiran su da Tunani. Amma wani lokacin ana kiran kwakwalwa da tunani ita ma, don haka ne sai a ce, ya fado cikin tunanina, ko ya mini yawo a tunani; wato surorin da suke cikin kwakwalwata sun fado mini, ko sun haskaka gareni, ko sun bayyana a gareni. Tunani kalma ce da ake gaya wa wanda yake amfani da bangarorin ruhinsa (ransa) yadda ya dace, idan mutum ya yi amfani da zuciyarsa, ko kwakwalwarsa ko hankalinsa to ya yi tunani ke nan. Kuma ana amfani da shi a kowane irin saken zuci ko saken tunani, ko saken kwakwalwa da mutum yake yi.
|