Allah MadaukakiDaya daga cikin siffar Allah da aka yi ta ja-inja a kanta ita ce Adalcin Allah, amma mu a takaice a nan zamu ce: Duk wani nau’in zalunci ya koru ga Allah, domin dukkan hanyoyi hudu da za a iya yin zalunci sun koru daga gareshi kamar haka: 1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa zalunci ba ne. 2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma kasa barin aikata shi. 3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma kasa barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa. 4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya kasance ya yi zalunci ne kawai don sha’awa da wasa. Dukkan wadannan siffofi sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna. Sannan haka nan Allah ba ya tilasta wa bayi aikin da ba zasu iya yin sa ba, kamar yadda ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani. Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a. Babban nauyin da yake kan baligi shi ne wajabcin ya san Allah madaukaki, bai halatta ba ya bi wani a kan haka ba koda kuwa babansa ne, dole ya yarda Allah daya ne, ta yadda da babansa ko malaminsa zai ce Allah sabanin haka ne, to ba zai bi ba. Cibiyar Al’adun Musulunci
|