Sayyid Khamna'iAMSA:A'a ni dai ban taba ganin irin wannan ganawa ba, amma dai ina sane da ita. Ina sane da cewa Jagoran ya kan sadu da mutane, a lokacin tafiyarsa ko kuma lokacin dawowa, wadanda sukan zo su gaishe cikin kaunar juna da girmamawa, shi ma kuma ya mayar musu da irin wannan gaisuwa tare da girmamawa a yayin da suke ganawar da kuma magana da juna. TAMBAYA:Shin ko za ka iya bayyana mana yanayi ayyukansa na kowace rana ko kuma na sati? Hakan kuwa saboda da dama za su so sanin yadda rayuwarsa ta ke, kuma kana daga cikin wadanda suke a matsayin da za su iya bayyana hakan? AMSA:To, daya da cikin ayyukan da yake yi dai kusan ko yaushe shi ne farkawa alal akalla awa guda kafin kiran sallar asuba, ya kan yi amfani da wannan lokaci wajen ibada da salloli. Daga nan kuma sai ya yi sallar asuba, a wasu ranakun kuma sai ya tafi hawa dutse, in kuwa bai tafi ba ya kan dan huta. Ya kan fara ayyukansa na rana ne da misalin karfe 8 na safe. Ayyukansa dai suna da yawa; daga cikinsu dai shi ne ganawa da jami'ai gwamnati, fararen hula da na soji, wadanda suka bukaci ganawa da shi kuma aka ba su lokaci na musamman. Wadannan jami'ai sukan zo da kuma gabatar da rahotanninsu, daga nan kuma Jagora mai girma ya kan bayyana musu abubuwan da ya kamata su yi. Irin wannan aiki dai ya kan kare zuwa wajen sallar azahar. Daya daga cikin abubuwan da ya kebantu da su shi ne ya kan yi sallolinsa ne a jam'i (tare da jama'a) koda kuwa sallar asuba ce da ya ke yi a gida. Ya kan yi sallar azahar ne kuwa tare da bakin da suka zo masa da kuma sauran ma'aikatan ofishinsa. A wasu lokuta ma wasu mutane, jami'ai da kuma malamai da suke son yin salla a bayansa sukan zo a daidai wannan lokaci. Bayan gama sallar azahar, ya kan shiga don cin abincin rana da kuma dan hutawa, kana kuma ya dawo ofis da misalin karfe hudu na yamma (a wasu lokuta ya kan ci gaba da ganawa da mutane). Haka nan zai ci gaba har zuwa lokacin sallar magariba, wanda ya kan yi ita ma tare da jama'a. Da daddare kuwa, mai girma Jagora ya kan yi karatu ko kuma sauraron labarai a talabijin ko kuma ya kasance tare da iyalansa. TAMBAYA:Ka yi magana kan karatu, shin wasu bangarori ne Jagora din yake irin wadannan karatun, baya ga labarai da kuma rahotanni na musamman? Shin akwai wani fage ne na musamman da yake karatun a ko yaushe? AMSA:E, lalle Jagora ya kan karanta littattafa da suka shafi fannin fikihu na musamman, kana kuma ya kan zauna da manyan malamai sau guda a kowani mako. A kowani sati ya kan gana da manyan malamai da mujtahidai a nan ofishin don tattaunawa kan mas'alolin da suke bukatuwa da a yi dubi cikinsu, kuma wadannan tarurruka sukan kasance masu amfani sosai. Baya ga haka kuma ya kan yi darasi kan wasu fannonin na daban kuma. TAMBAYA:Shin wadannan tarurruka (da yake yi da malamai) akan yi su ko yaushe ba tare da fashi ba? AMSA:Kwarai kuwa akan yi su ko yaushe ba tare da fashi ba, kuma shekara da shekaru aka yi ana yinsu, sai dai kawai lokacin da ba ya nan a birnin Tehran (idan ya yi tafiya). TAMBAYA:To ya ya sauran bangarori na ilmi kuma, kamar su adabi?
|