Mushafin Fadima (a.s)Mece Ce Gaskiyar Mushafin Fadima (a.s) Akwai maganganu masu yawa da ake yi game da abin da ake kira da mushafin Fadima (a.s) wanda ya zo a cikin ruwayoyi, kuma makiyan Shi'a sun yi amfani da wannan wurin ganin sun bata sunan su ta hanyar tuhumar su da cewa; suna da wani Kur'ani mai suna mushafu Fadima. Sai dai wannan tuhuma ce ta bata suna, maras wata kima da tushe da ba ta da asasi, domin da zarar mai bincike ya koma wa ruwayoyin Ahlul Baiti (a.s), to zai samu abin da yake karyata wannan kagen cikin sauri, sai dai duk da haka an samu wasu masu taurin kai da ba sa iya barin nuna kiyayyarsu ga tafarkin alayen manzon Allah har abada da suka ci gaba da wannan kagen. Mushafi a lugga yana nufin: Tattararrun takardu, kamar yadda farra'u ya kawo; Islahul Mandik: 354, da kuma Sihah: 4/1384, Jauhari. Abul Hilal yana cewa: Banbanci tsakanin littafi da mushafi shi littafi yana iya kasancewa da takarda daya rak, amma mushafi ba ya yiwuwa sai da takardu masu yawa. Mushafin Fadima (a.s) wani lallashi ne da ta'aziya da sayyidina Jibril (a.s) yake yi wa Fadima (a.s) da ta kasance tana jin maganarsa bayan wafatin manzon Allah (s.a.w), kuma imam Ali (a.s) yana rubutawa, sai aka ambaci wannan tattararrun maganganun da take ji da Mushafin Fadima (a.s). Kuma wasiyyan manzon rahama (a.s) kuma halifofinsa sha biyu tun daga Kuma shi ne littafin da musulmi suka rubuta na farko bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) domin sayyida zahara (a.s) ta rasu 3 Jimada Ulam 11, H, kuma ba a rubuta wani littafi ba a cikin wannan dan tsakanin sai mushafinta, kuma wannan yana nuna mana a fili cewa; lamarin ba shi da wata alaka da Kur'ani kamar yadda masu gaba da gidan Annabi (s.a.w) suke neman likawa. Sannan babu mamaki don Jibril (a.s) ya yi mata magana kamar yadda yake yi wa Maryam, domin ita ma Muhaddisa ce, ba Annabi ba, Biharul Anwar: j 39; 55, da kuma 39; 79. Mala'ikun Allah sukan yi wa bayinsa magana kamar yadda suka yi wa babar Musa (a.s) da matar Annabi Ibrahim Sara, da makamantansu. Don haka babu mamaki ga mai basira don sun yi wa shugabar matan talikai magana wacce ta fi wadancan matan duka kima da matsayi wurin Allah madaukaki, Ilmuddiraya: Subhani; 20. Mushafin Fadima (a.s) ya kasance ne kamar yadda ruwayoyi suka zo cewa; Fadima (a.s) ta samu kanta cikin matukar damuwa bayan wafatin babanta, sai Allah ya umarci mala'ika Jibril da ya rika yi mata ta'aziyya, yana ba ta labarin inda babanta yake, da matsayin da ya samu, da kuma makomarta da ta 'ya'yanta har zuwa ranar kiyama. Sai ta 1- Ya ninka Kur'ani sau uku yawa
|