Hadisin Manzila6. Ranar Gadir Khum Duba littattafai kamar haka; Manakibu Ali bn Abu Dalib: 151, da Kifayatud Dalib: 212. Sannan malamai da masana hadisi masu yawa sun tafi a Ga mai son yin adalci babu wani abu da ya buya na manufar wannan hadisin da kuma ma'anarsa Na farko: Matsayin imam Ali (a.s) mai daraja da girma. Na biyu: Cancantarsa ga halifancin Annabi (s.a.w). Na uku: Bayyana cancantarsa da matsayinsa na kasancewarsa halifan Annabi (s.a.w) ban da annabci, musamman a fili ya zo a cikin ruwayar Ahmad cewa; Ba zai yiwu in tafi ba, sai kai kana halifana. Na hudu: Shelanta cewa duk wani matsayi da Haruna (a.s) yake da shi gun Musa (a.s) to shi ma Ali (a.s) yana da shi gun Annabi (s.a.w) sai dai annabta kawai. Da wadannan dalilai ne ake kiran wannan hadisin da "hadisi manzila" wato; "Hadisin Matsayi". Domin duk wani matsayi na Annabi Harun (a.s) gun Musa (a.s) kamar 'yan'uwantaka, da wazirci, da halifancin al'umma bayansa, da ilimi, da tarayya wurin isar da sako da kira, kamar yadda ya tabbata a yar nan ta Surar Daha: 29/32. Duk sun tabbata ga Ali (a.s) gun Annabi (s.a.w) a wannan hadisin. Kamar yadda yake bisa ka’idar nan ta ludufin Allah da tausasawarsa ga bayinsa ya zama wajibi a cikin al’umma a samu wanda zai shiryar da ita zuwa ga mafi maslahar rayuwarta ta duniya da lahira, wannan ludufi na Allah kuwa yana nan a kowane zamani da kowane waje, don haka ne ya zama cigaban wannan ludufi yana kasancewa ne da samun wasiyyai da sukan biyo bayan annabawa domin gudun kada al’umma ta karkatar da wannan sako ta gurbata shi, kuma da bukatar da al’umma take da ita na neman haskakawa da iliminsu da haskensu, hada da cewa yana daga ayyukansu su kare shari’a daga gurbata. Ana kawo dalilai game da wajabcin sanya imami ga mutane bayan wucewar Annabin rahama (s.a.w) kamar haka: 1. Sanya imami ludufi ne na Allah, shi kuma ludufi wajibi ne ga Allah 2. Samuwar imami shi ne maslahar al’umma, samar da maslaha ga bayi wajibi ne ga Allah
|