Annabcin Annabi Musa (a.s)A bisa zahiri ana iya cewa da’awar Annabi Musa (a.s) ba ta shafi wasu ba, in banda Banu Isra’il, kuma daya daga cikin dalilan da suke tabbatar da hakan shi ne; yayin da ya ga wasu mutane suna bautar gumaka bayan an tseratar da Banu Isra’il, sai mutanensa suka ce: Ka sanya mana ubangiji kamar yadda suke da shi, Annabi Musa (a.s) bai amsa wa mutanensa ba, sannan kuma ya kwabe su kan cewa abin da wadannan mutanen suke yi bata ne. Sannan kuma babu wani dalili da muka samu a kan cewa ya gargadi wadannan mutanen kan abin da suke yi na bautar gumaka kamar yadda ya gargadi mutanen fir’auna, domin su ba ya bukatar tseratar da Banu Isra’il daga hannunsu. Sai dai duk da hakan abin da muke kawo wa na rashin samun dalili a Sannan babu wani tarihi da ya zo da labarin cewa; Annabi Musa (a.s) ya kira wasu mutanen bayan halakar da fir’auna da mutanensa, abin da ya zo mana game da shi yana bayanin wahalhalun da ya sha ne bayan sun kubuta daga fir’auna, ta yadda mutanensa (a.s) suka ki biyayya gareshi ta shiga garin da aka umarce su, har sai da Harun (a.s) ya rasu, kuma Musa (a.s) ya rasu bayansa da shekara daya, sannan sai Annabi Yusha’u ragowar na gari kuma wasiyyin Musa (a.s) ya karbi jagorancin al’umma ya yaki mutane masu tsaurin kai, Allah ya yi musu budi a hannunsa. A cikin wannan halin na dimuwa da suka shiga a cikinsa ne Annabi Musa da Harun (a.s) suka rasu, kuma wannan halin na dimaucewa da suka yi, ya dauki shekaru arba’in ne kamar yadda Allah madaukaki ya yi musu alkawarin wannan dimuwa a cikin wannan muddar. Duba, Surar Ma’ida: 21-22. Hada kuma da cewa babu kayan sadarwa cikin sauki a wannan zamanin, babu hanyoyin isar da sako kamar yadda ya kamata, don haka sanya annabcinsa ya kasance zuwa dukkan duniya lamari ne wanda yake ba mai yiwuwa ba. Hada da cewa; al’ummun wannan lokacin suna cikin tsananin makantar kabilanci da bangaranci, ta yadda zuwan wani bare a cikinsu da sunan sakon Allah, yanayinsu ba zai karbe shi ba, don haka ne hikimar Allah madaukaki ta fi dacewa da aiko kowane Annabi (a.s) zuwa ga mutanensa ne. A bisa zahiri wannan yana iya tabbata idan muka duba kissar Annabi Musa da Hidir (a.s) wanda aka hada tsakaninsu kuma Musa (a.s) ya amfana da ilimomi da sirrori daga tafiyarsu tare; Kahafi: 65-66. Wannan yana iya nuna yiwuwar samuwar annabawa da yawa a wurare mabambanta ko wuri daya a cikin zamani daya, kamar dai Annabi Ibrahim (a.s) da Annabi Lud (a.s); Ankabut: 31-32. Amma bahasi na biyu mai cewa; shin shari’ar Musa (a.s) ta game dukkan mutane ne ko kuwa kawai ta hau A nan ma wasu sun yi da’awar cewa; ta game dukkan al’ummar duniya ne, wannan kuwa bisa dogaro da zahirin cewa; an rubuta masa komai a cikin allunan da ya karbo. A’arafi: 145. Da kuma kasancewar littafinsa haske ne ga masu takawa; Anbiya: 48. Da shedar aljanu a Sai dai idan muka duba hujjoji masu yawa da suke cikin Kur’ani mai daraja zamu ga wannan da’awar da aka yi ba zata iya tabbata ba, musamman cewa; wani wanda ba daga cikin Banu Isra’il ba zai iya amfana daga littafin Musa (a.s) koda kuwa sakonsa bai game har da shi ba, ga shi mu ma yanzu musulmi amma muna amfana daga Attaura ta fuskacin wa’azozinta koda kuwa ba mu amfana ba ta fuskacin hukuncin da yake kunshe cikinta. Sannan kuma idan mun duba zahirin ayoyi masu yawa karara sun nuna cewa wannan sakon ya kebanta a shar’ance ga Banu Isra’il ne; muna duba ayoyi kamar haka: mai nuna cewa shi shiriya ne ga Banu Isra’il; Gafiri: 53. Da mai nuna cewa; an saukar wa Banu Isra’il hukuncin kisasi; Ma’ida: 32, 44, 45. Da mai nuna an ba su littafi da hukunci; Jasiyat: 16. Da wasu masu yawa da suke nuna su aka saukar wa da littafin karara a fili kamar haka: bakara: 121, 144, An’am: 20, 114, Ra’ad: 36, Ankabut: 47. Akwai mai nuna cewa an saukar wa da Banu Isra’il littafi amma ba a saukar ga mushrikai ba a yankin larabawa kamar haka; An’am: 156-7. Don haka hatta da ayoyin da suka yi maganar saukarsu ga mutane ana iya fassara su da abin nufi da su, su ne Banu Isra’il, domin wasu ayoyin suna fassara abin nufi da wasu ayoyin. Don haka wannan yana iya tabbatar mana da cewa; shari’ar Annabi Musa (a.s) kamar sakonsa na kadaita Allah ne, wanda bai kasance ya shafi dukkan halittun mutanen duniya ba!. Hafiz Muhammad Sa'id Saturday, September 12, 2009
|