Babar Babanta!



Abu Jahal (L) ya motsa yana mai cewa ina ganin ku kashe shi kawai. Sai wani ya ce: Yaya zamu yi da fushin Bani Hashim da takubban dakarunsu?. Abu Jahal ya ce: Amma yadda za a yi shi ne, kowanne daga cikinku ya dake shi da takobi dukan kwaf d'aya sai ku yi musharaka a jininsa gaba d'aya ta yadda Bani Hashim ba za su iya d'aukar fansa ba sai dai maganar diyya.

Da Fad'ima ta ji wannan magana sai zuciyarta ta cika da tsoro a kan Babanta, ta lizimci wajan, ta k'i barinsa, idanunta suna kula da hanya har sai ta ga Babanta ya b'ullo da sauri sai ta gaya masa duk abin da K'uraish suka yi  na makirci da kaidi.

Sai ya gaya mata cewa kada ta damu: “Ki tabbata ya ‘yata Allah ba zai tab'a ba su dama a kan Babanki ba”. Annabi ya wuce masallaci har sai da ya shiga ya wuce mutanen da suke mitin a kansa domin kashe shi, sai suka yi shiru suka rufe idanunsu saboda abin da suka gani a fuskarsa na haiba da kwarjini, suka mance abin da suka yi ittifaki a kansa d'azu, har sai da Manzo (s.a.w) ya tsaya a kansu ya d'auki k'asa jimk'i d'aya ya watsa a kansu yana mai cewa: “Fusaku sun muzanta”.

Sannan ya fuskanci Ka’aba ya yi salla ga Allah mad'aukaki (s.w.t) a kusa da su, Fad'ima (a.s) tana tsaye tana ganinsu ba wanda ya motsa daga cikinsu kamar ba wanda ya gan shi, yayin da ya gama sallarsa da munajatinsa sai ya rik'e hannun ‘yarsa suka tafi gida tare!

Haka nan ta sami wani k'unci mai yawa na abin da ta gani wata rana, Babanta yana salla a Ka’aba, ga Abu Jahal (L) da wasu daga K'uraishawa kamar su Asi d'an Wa’il Assahami da Haris d'an K'ais Assahami (L) suna yanka rak'umi. Sai Abu Jahal da Umayya d'an Khalf (L) suka waiga suka ce da yaransu: Waye zai zo mana da mahaifar rak'umin Bani Saham sai ya d'ora shi a kan bayan Muhammad! (s.a.w) idan ya yi sujada?

Wannan tunani ya yi wa wasunsu daidai Uk'uba d'an Abi Mu’id' (L) da Utba da Shaiba ‘ya’yan Rabi’a (L) suka tashi suka d'auko tunbi da mahaifar suka d'ora kan k'afadun Manzon Allah (s.a.w) yana mai sujada.!

Fad'ima (a.s) ta ga abin da aka yi wa Babanta sai ta gaggauta tana mai jin zogi da bak'in ciki mai tsanani a kan abin da ta ga ni, hawayenta suna kwarara a kan kumatunta, saboda haka sai ta bayar da duk k'ok'arinta wajan ganin ta kawar da wannan daud'a daga kafad'un Babanta (s.a.w), Annabi mai girma Uba mai rahama ya d'aga kansa yana kallon ‘yarsa Fad'ima (a.s) idanunsa cike da rahama da tausayi da k'auna da yarda da bege gareta, tare da dukkan abin da zuciya zata iya nuna wa na nutsuwa da tabbata da hak'uri, sannan sai ya rik'e hannayenta tsarkaka ya tattaro ta zuwa k'irjinsa mad'aukaki ya ce: “Mamakin yadda kika zama babar babanki da wuri haka Ya Fad'ima”[4].

Bai bar wannnan waje mai daraja ba tare da ita, wajan da kafiran K'uraish suka b'ata da daud'a sai da ya d'aga hannayensa zuwa sama yana mai addu’a yana cewa: Ya Allah! ina kai k'arar Abu Jahal (L) da Utba da Shaiba ‘ya’yan Rabi’a (L)  a wurinka ka. Ya Allah! ina kawo k'arar Umayya d'an Khalf (L) da Walid d'an Utba (L) da Ukuba d'an Abi Mu’id' (L) da…[5].

Kada ka so ka ga irin farin cikin Fad'ima ‘yar Manzo (a.s) a wannan rana sakamakon irin matsayi da ya ba ta na wannan kalma ta (Babar Babanki) da ya d'aukaka ta zuwa gare shi, kamar yadda ta iya sanya wa a ran Babanta (s.a.w) a wannan ranar da aka samu had'uwa a ruhi guda biyu da had'uwar k'anshi da k'anshi, kuma haske da haske, cewa ruhin Baban (s.a.w) mai kira zuwa ga Allah ya samu sanarwa daga ruhin ‘yar mai neman ta zama uwa ga Baban (a.s) cewa ruhinta ruhi ne mai cike kuma k'unshe da tausayi irin na uwa ga uban kuma kariya mai k'arfi mahalarciya a kowane abu da ya faru ga uban (s.a.w), wanda sau da yawa irin wad'annan abubuwa suka yawaita bayan K'uraishawa sun samu dama da wafatin Abu Talib!!, sanarwar da ruhin uban ya samu daga ruhin ‘yar shi ne cewa ita uwa ce, don haka ta cancanci wannan kalam ta Babar Babanta. Hafiz Muhammad Sa'id, An rubuta a 2003, An gyara, August 05, 2009


[1] A lokacin shekara ta goma da aiken manzon Allah (s.a.w) ne, bayan fitowa daga Tsarin na ba jimawa, kuma kusan shekarun sayyida Zahara (a.s) takwas ke nan.

[2] Buhari: 9/244. Al'isaba: 4/282. Nuzhatul Majalisi: 2/196. Kashful Gumma: 1/360.

[3] Ma'aikin Allah (s.a.w) ya yi wa 'yarsa wannan lak'abin; duba al'isaba fi tamyizis sahaba: 4/377. al'isti'ab: 4/380. Mak'atilul D'alibiyyin: 3/132.

[4] Hashiya, shafi: 67.

[5] D'abari: Zakha'irul Uk'uba, shafi: 47

 

 



back 1 2 3