Tattaunawa Ta Takwas



Ina ganin ya kamata  Imam Ali (a.s)  alal akalla ya ci darajar cewa shi ma sahabi ne a wurinka idan dai har kana girma sahabbai din, domin wannan maganarsa ce.

 Kai manzon Allah ya dawo da mukamu Ibrahim daga inda jahiliyya suka canja masa wuri ya mayar da shi wurin da Annabi Ibrahim (a.s) ya sanya shi da umarnin Allah amma a lokacin halifa na biyu Umar dan Khaddabi sai ya dawo da shi inda jahiliyya suka ajiye shi.  Allah yayi hisabi tsakanin ka Umar(RA) An yi wa Ali (a.s) magana ya sake ajiye shi wurin da Annabi (s.a.w) ya sanya shi amma ya ce yana gudun kada a dauki Ka'aba wasa.

Bahasinka yana nuna jahilci a ciki yayin da kakan yi fushi ka yi zagi babu dalili, kana kiran kanka Ahlussunna amma kana tsananin kin abin da Ahlussunna suka rubuta da kansu idan aka gaya maka.

Wannan lamarin ya faru, kuma duk da hujjojin Ahlussunna a wurinka ba hujja ba ce, wannan yana nuna ke nan bahasi da kai ba shi da amfani tun da ba ka yarda da dukkan abin da Ahlussunna suka rubuta ba. Amma domin ilmantarwa ka duba:

Tarihin Ya'akubi: j 2, shafi: 149, wannan ya faru a shekarar 17 Hijira. Da Suyudi a Tarihul Khulafa. Da: Dumairi a Kitabul Haiwan a Kalmar Diik. Da: Alkamil fit Tarih, Ibnul Asir: 2/ 537. Dabakat Ibn Sa'ad 3/ 204. Sharhu Nahajul Balaga: 3/ 113.

Sheikh Naja Atta’i yana mai kawowa yana mai kafa sheda da wadannan abubuwan da muka kawo maka na littattafai cewa: Umar ya canja mahallin Mukamu Ibrahim (a.s) ya dauke shi daga inda Annabi Ibrahim da Isma'il (a.s) da manzon Allah (s.a.w) suka sanya shi ya mayar da shi inda Jahiliyya suka sanya shi.

Sannan; kuma Ibn zubair ya dawo da shi inda manzon Allah ya sanya shi, amma kuwa Abdulmalik ya sake dawo da shi inda Umar ya mayar da shi wato wurin da jahiliyyar Kuraishawa suka sanya shi bayan mamayar ruwa da gyara Ka’aba.

Amma duk abin da ya fi ba ni mamaki da kai shi ne inda ka nuna ba ka son Umar soyayya ta gaskiya, domin duk inda ya yi magana idan ya nuna yana da waliyyi wato sayyidi Ali (a.s) sai in ga ka ki yarda da Umar, wannan yana nuna son karya ga Umar ko ma sahabbai, domin da kana son su da ka dauki maganganunsu.

Amma wannan ya sake nuna mini abin da na gaya maka shekarar da ta gabata har ya sanya na tsayar da tattaunawa da kai domin ba ta da amfani.

Inda ka yarda da maganar sahabbai da littattafan Ahlussunna da tattaunawa da kai ta yi amfani!



back 1 2 3 next