Tattaunawa Ta Bakwai



Wannan lamarin ya sanya farkon digon ba na rigimar halifa na uku tsakaninsa da Hafsa da A'isha har ya kai ga A'isah ta kafirta shi da halatta jininsa da la'antarsa!! Wannan lamurran duk suna nuna cewa Zahara (a.s) ita ce ke da gaskiya kan wannan lamarin.

Sannan kada ka manta al'amarin bai tsaya a gado ba, har ma da dukiyarta da aka kwace ta gonar Fadak, wacce magana a kanta tana da tsayi, kuma duk da Ummu Aiman da manzon Allah ya yi sheda gareta, da kuma Ali (a.s) da 'ya'yanta da makusanta sun sheda da cewa manzon Allah (s.a.w) ya ba ta, amma aka hana ta. Alhalin Jabir bn Abdullah ya gaya wa halifa na farko cewa manzon Allah ya yi mini alkawarin zai ba ni dukiya idan ta zo daga Baharain sai ya ba shi bai nemi sheda ko rantsuwa daga gareshi ba.

Don me ya sa 'yar Annabi (s.a.w) ba ta samu wannan karar ba koda kuwa saboda babanta ne: Duba kissarsa da Abubakar a cikin Majama'uz Zawa'id na Haisami: j 5, shafi: 630, H 9772.

A kalla a shar'ance idan ba a yarda da shedunta ba masu wannan daraja da tsarki to sai halifa ya rantse, idan kuwa ba haka ba, babu hujjar kwace mata wannan gona saboda ka'idar nan ta "Yadd" da ta shahara a musulunci.

Amma da kake zargin mijinta da ya kyale irin wadannan lamurra suka faru ka sani: Manzon Allah (s.a.w) ya gaya Imam Ali (a.s) cewa zai hadu da bala'o'i bayansa amma ya yi hakuri kada ya sanya takobi, kada ka manta cewa; shi ne Harunan Muhammad (s.a.w)! Sannan kuma ya yi magana kamar yadda Haruna ya yi yayin da yake cewa: "Innalkaumas tadh'afuni wa kadu yaktulunani…": Yana mai kuka a kabarin manzon Allah (s.a.w). Sannan kuma 'yar manzon Allah ba kasuwa ta tafi ba aka dake ta kamar yadda ka kawo kana mai isgili da lamarin, an balla kyauren gidanta ne aka shiga, an buge ta a ciki ta yi bari, an yi mata bulala da mari.

Abin mamaki wannan mamaya ta zo a cikin irin wadannan littattafai na AhlusSunna amma kana cewa; Sayyida Zahara (a.s) ta tafi kasuwa ne sai aka yi mata duka a can. Mu sanya ma ta tafi kasuwa ne sai aka yi mata duka a can don me za a doki 'yar manzon Allah (s.a.w) alhalin bai yi kwana uku da rasuwa ba, da wanne zata ji da rashin uba gatanta ko da duka da hauri da bulala da mari!

Ka sani Ibn Kutaiba madogara gun Sunna da mai biye masa Dabari sun ruwaito cewa: Halifa na farko Abubakar Dan Abi Kuhafa yana fada yayin da zai mutu ya yi nadama ina ma dai bai sanya an kai mamaye da samame gidan Sayyida Zahara (a.s) ba". Ina ma dai bai yi mulkin al'umma ba, ina ma dai bai …., da kin bin Usama saboda la'anar da aka yi wa wanda ya ki bi…, da kin tsayar da hakkin kisa da zina kan Khalid…" da sauransu. Duba Ibn Kutaiba Addinuri a littafin Imama Was Siyasa yana mai cewa: Abubakar ya ce: Ya yi nadamar abubuwa uku da ya sani da ya bar su bai yi ba, kuma kuma da ya bari da ya sani da ya yi su, uku kuma ina ma dai ya tambayi mazon Allah (s.a.w) game da su: sai ya ambaci ukun da ya yi nadamar yinsu kamar haka:

Na daya: Mamaye gidan zahara (a.s) koda kuwa an kulle shi a kan yakar sa ne. Na biyu: Ina ma dai bai karbi shugabanci ba ya ba wa Umar ko Abu Ubaida ya huta. Na uku: Ina ma dai ya kashe Fuja'atus Salami ko ya sake shi bai yi masa ukubar da ya yi masa da wuta da kunyatawa. Sai kuma ya kawo wanda ya so a ce bai bari ba ya yi su kamar haka; Na daya: Ina ma dai ya kashe Ash'as dan Kais. Na biyu da na Uku: Ina ma dai da ya tura Khalid bn Walid Sham ya tura Umar Iraki. Amma ukun da ya so a ce ya tambayi manzon Allah (s.a.w); Na daya: Ina ma dai ya tambaye shi waye shugaba bayansa don haka babu wani mai jayayya. Na biyu: Ina ma dai ya tambaya ko Ansar (mutanen Madina) suna da wani rabo a mulki. Na  uku: Ina ma dai ya tambaya game da gadon 'yar dan'uwa da amma.

Haka nan ma Ibn Abil hadid bahanife ya kawo yana mai nakaltowa daga Mubarridu yana mai fadin wannan lamarin da muka kawo daga Ibn Kutaiba, har da karin cewa: Ina ma dai ya tambayi waye shugaba bayan Annabi (s.a.w) da kuma haddi, da cin yankan Ahlul Kitabi. Kuma ina mai dai bai mamaye gidan Fadima ba, da kin bin rundunar Usama, da barin Ash'as. da kuma fadin Ina ma dai ya yi wa Khalid bn Walid kisasi da kashe Malik bn Nuwaira, da kuma ina ma dai ya kashe Uyaina dan Hasin da Dalha dan Khuwailid.

A yanzu kana cewa ka fi Abubakar sanin abin da aka yi wa 'yar manzon Allah (s.a.w) bayan abin da ya fada, ko kana nufin a wurinka Abubakar ba adali ba ne da ba zaka sallama wa maganarsa ba!



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next