Tattaunawa Ta Uku Haka ne mumini ba ya dawwama amma da sharadin ya mutu muminin, ba wanda ya take maganar Allah da Manzo (s.a.w) ya ki karba ba, alhalin ya san daga garesu take kuma ya ki imani da ita, kafircewa ayar Allah (S.W.T) karara babu wani tawili bisa sani kamar kafircewa dukkaninsa ne, kuma ayar nan ta ط£ظپطھط¤ظ…ظ†ظˆظ†ط¨ط¨ط¹ط¶ ط§ظ„ظƒطھط§ط¨... tana nuni da haka ne. Amma batun cewa Buhari bai fitar da wannan hasidin ba na sakalain; Littafin Allah da Alayen manzonsa, Na yarda da cewa bai fitar da shi ba, amma Mustadrak ya fitar da shi a matsayin abin da Buhari ya yarda da shi amma bai kawo shi a littafinsa ba. Wato hadisin bisa dokokin fitar da hadisi gun Buhari ya inganta amma ba a san dalilin da ya sa bai kawo shi ba a sahihinsa. Sannan kuma a yanzu da zan tambaye ka mene ne abin da Manzo (s.a.w) da sahabbai suke a kai kana ganin zaka iya ganowa bayan faruwar duk abin da muka fada a baya, alhalin kowa yana ganin cewa na sa ne daidai, ingantacce! Sannan kuma mun fadi cewa Manzo (s.a.w) ya ayyana halifofinsa masu shiryarwa. Su goma sha biyu. Wannan kuwa bayan dalilai daga littattafai, muna iya karawa da cewa; hankali ba zai iya rashin kunyar jingina rashin hikima ga mahalicci da manzonsa (s.a.w) ba, na abin da wasu suka raya cewa Manzo (s.a.w) zai ce a bi wadannan halifofi sannan sai ya ki ayyana su ya bar mutane cikin dimuwa ba su san su ba! don haka ne ma ka ga wasu suna ta kokarin hada su sun kasa!!! Suna gudun na Manzo (s.a.w) domin bangarancin Umayyanci ko mazhabanci alhalin sun kasa hada nasu. Amma da kake ganin yaya wasu zasu so manzon rahama sanna su ki 'ya'yansa da zuriyarsa da alayensa sai in ce maka: Ka sani babu alaka tsakanin son mutum da son â€کyan’uwansa, ba dole ba ne don ka so mutum hatta da â€کya’yansa ka so su, ka duba Manzo da Abu lahab, da Annabi Nuhu (a.s) da dansa, don haka fassara Kur’ani da ra’ayi kamar yadda na gaya maka ba abin da zai kai mu sai bata, Manzo ya fassara ma’anar zulkurba, da ma’anar Ahlul Bait, ya fassara ma’anar nisa’ana, abna’ana, amfusana, da duk wani abu da ya zo a Kur’ani. Da mai fassara zai buda lugga ne da sai ya fassara wadannan ayoyi bisa ra’ayinsa, da wannan kuwa sai ya fada cikin halaka! Amma da kake tambayar makomar wadanda suka mutu a lokacin Annabi(SAW), ga shi kuma babu mazhabar Ahlul Baiti (a.s) alokacin tun da Annabi (SAW) na da rai, da cewar Addini ya cika kafin wafatin Annabi (SAW) koko? Ga kuma Kur'ani da hadisai na Manzon Allah(SAW)? Sai in ce maka: Mazhabar Ahlul Bait (a.s) ana ba ta suna ne na mazhaba sakamakon abin da ya faru a duniyar musulmi, kamar yadda Manzo (s.a.w) ya ambaci jama’a zata kasu gida 73 kamar yadda ka kawo a baya, kuma kowane daga ciki yana da suna, amma daya daga cikinsu duk irin sunan da aka ba shi koda mazhaba aka kira shi, ko Shi'a’ ko rawafidawa, ko imamiyya, ko ja’afariyya, yana nan a matsayin jama’a mai tsira matukar dalili ya tabbata a kan hakan. Don haka sanya suna baya cutarwa ko shi mazhabin ne ya ba kan shi sunan ko kuma makiyansa ne suka ba shi. Sannan kuma addini ya cika: kuma ayar kammala shi ta sauka a ranar Gadir Khum bayan yi wa imam Ali bai’a sabanin yadda wasu suka sanya siyasa game da saukarta. Amma kokarin da kake yi na hada alaka tsakanin fitar da Ummu Salma daga cikin Ahlul Baiti, da mas'alar haramta sadaka, hada da kokarin fassara Alayensa da aali Akilu, aali Jaafar, aali Abbas":
|