Tattaunawa Ta FarkoSanannen abu ne cewa mutanen karni na daya da na biyu da na uku ba su san wadannan mazhabobi ba, sun san su ne bayan an soke sauran mazhabobi a karni na hudu kuma aka rushe saura suka rusu, amma wannan mazhaba ta Ahlul Bait (a.s) da tun ranar da manzon Allah (s.a.w) ya yi wafati aka fara yakar ta, amma kuma ta zauna daram har yau, alhalin ba ta taba samun tallafi daga masu mulki ba a wadancan zamuna. Sannan zabar Ahlul Bait (a.s) a matsayin wadanda Shi'a suke biyayya ga tafarkinsu ba yana nufin kin waninsu ba, don saudayawa wasu sun dauka biyayya garesu tana nufin kin waninsu na daga sahabbai, don haka ne ma suka dauka Shi'a ba sa son sahabbai alhalin idan maganar sahabbai ce to ina tabbacin ba na tsammanin Shi'a sun fadi wani abu da ya fi wanda ahlussunna suka fadi game da su muni. Wannan maganganu ne da suka zo a littattafai a wurare masu yawa daga littattafai ingantattu na ahlussunna wadanda suka yi nuni da hakan. Kada mu manta cewa Allah (S.W.T) da manzonsa su ne suka fifita Ahlul Bait (a.s) saboda sun san sun fi sauran bayi takawa da ilimi da sanin Allah da siffofi madaukaka kuma su ba sa sabo. In ba haka ba, da sun kasance kamar sauran mutane wajan kasancewarsu ba hujjar Allah ba ne a kan bayinsa. Mu sani ma’aunin fifiko ba yana cikin kasancewar wane sahabi ba ne ko tabi’i: musulunci ya zo da daidaito da nuni da cewa wanda ya fi takawa shi ne ya fi a wajen Allah. Wani abin lura ma shi ne; hasali ma Ahlussunna sun tafi a kan cewa wanda ya yi imani ba tare da ya ga manzon Allah (s.a.w) ba to ya fi sahabbai 50 darajar lada. (Koda yake wasu daga malaman Ahlussunna suna da wasu tawili kan suhuba, wannan kuwa kiyasi ne da aka yi ta rushe addinin Allah da shi) wannan yana nuna ke nan duk wanda ya yi imani a wannan zamani yana lada daidai da sahabbai 50 ne a bisa abin Ahlussunna suke kai, amma duk da haka a yau mumini ba hujja ba ne na Allah kan talikai. Wani abin mamaki sahabbai sun maimaitawa manzon cewa sun sha wahalar Badar da Uhud da Hunain da sauransu amma duk da haka ya maimaita musu sau hudu cewa mutanen da zasu zo bayansu su yi imani sun fi su lada sau hamsin. Wannan kuwa ya zo a cikin littattafai kamar Sunan Abu Dawud, Majma’azzawa’id, Dabarani, Kanzul Ummal. Wadanda suke manyan jagorori daga malaman Ahlussunna. Don Allah in tambaye ka mana Ya kai mai musun wilaya da tafarkin Ahlul Baiti (a.s); shin ka taba jin hadisi wanda yake ingantacce ne da duk malamai suka tafi a kansa yana cewa; Wanda ya mutu ba shi da bai’a ga imaminsa ya yi mutuwar jahiliyya!? Kuma shin ka taba tunanin waye imamin zamaninka!? Idan ka gano shi da wace hujja zaka bi shi alhalin Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) ba su ce a bi shi ba!! Idan kuwa kana da hujja sun ce ka bi shi to ka kawo ta!! Ka sani kamar yadda muka sha fada a baya ne cewa; Addinin nan ba gado ba ne, dan hujja ne; kuma duk inda gaskiya take to ita ya kamata mu bi. Ni na kasance ina da kananan shekaru a lokacin da nake koyar da Littafin Muwatta’ ta Maliku, amma na ga cewa akwai dalili mai karfi da ya fi nawa wanda ya sanya ni bin tafarkin Ahlul Bait (a.s). Don haka duk inda hujja take nan zan bi, kuma idan wani ya kawo hujja da tafi tawa karfi to zan bi abin da ya kafa mini hujja. Ya kai mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s) Ka sani ni da kai ba ma nan yayin da manzon Allah (s.a.w) ya yi wasiyya, kuma ba ma kusa da tafkin Gadir lokacin da aka yi wa Imam Ali (a.s) bai’a, kuma ba ma nan lokacin da ya yi wafati. Amma duk labaran abin da suka faru tun daga farkon wahayi har karshensa suna cikin littattafai, don haka abin da ya inganta daga garesu hujja ce mai karfi a kaina da kuma a kanka, ka sani mafi karfin hujja ita ce wacce ta futo daga bakin mai gaba. Wannan ne ya sanya fifikon Ahlul Bait (a.s) ya fito a fili, domin ya fito daga masoya da makiya da masu musuntawa kuma ya cika duniya. Hafiz Muhammad Kammala gyarawa 01 /July/ 2009
|