Tattaunawa Ta Farko



Shi'a ba sa ganin waninsu wanda ba kan mazhabar Ahlul Baita suke ba a matsayin mutane masu kiyayya da gaba da Ahlul Baiti (a.s), abin da muke cewa shi ne su ba kan mazhabar Ahlul Baiti (a.s) suke ba. Wannan kuma wani abu ne a fili, kowanne daga ma’abota mazhabobi kamar Malik da shafi’i da abu hanifa da ibn Hambal, da sauransu yana da mazhaba kuma yana da mabiya, tayiwu ka samu wani yana bin Malik kuma ba ya bin shafi’i, ko ibn Hambal har ma ya ga ibada kan fatawarsu ta baci a wata mas’alar, amma kuma wannan ba yana nufin ba ya son su ba.

Don haka rashin biyayya ga tafarkin wani ba yana nufin kinsa ba, kuma bana tsammani wani yana iya shaida ga Shi’a da cewa suna da wannan ra’ayi.

Amma idan kuma ana neman kafa dalili ne a kan wace mazhaba ce tafi kowacce karfin dalili, kamar yadda wasu suke kawo wannan tunani su fassara shi kuma su dara shi bisa kan hadisin rarrabuwa gida 73; (wanda yake nuna cewa jama’a 72 da biyu cikinsu zasu zama garwashen wuta) Sai mu ce ita ce mazhabar Ahlul Bait (a.s), domin su ne wadanda littattafai ingantattu na Shi'a da Sunna kamar sahihul Buhari da Muslim da sauransu, suka tafi akan cewa manzon rahama (s.a.w) ya yi wasiyya da bin su, yayin da ya bar mana Littafin Allah (S.W.T) da Ahlul Bait (a.s). kuma ya yi umarni da mu yi riko da tafarkinsu, sannan kuma wani abin alfahari da jin dadi wanda wannan addini yake dauke da shi babu wani abu da zai shiga maka duhu sai da aka yi bayaninsa, kamar su waye Ahlul Bait (a.s) sai da Manzo (s.a.w) ya nuna su kuma duniya ta yi shaida da haka. Yayin da manzon rahama (s.a.w) ya kore Ummu Salama matarsa daga kasancewa cikin matsayin Ahlul Bait (a.s), Kuma tafsirai sun yi shaida da hakan kamar fakhrurrazi da Durrulmasur na Suyudi, kai hatta da Ibn Kasir. Haka nan ma Sunan Tirmizi. Da sauran manyan littattafai na Ahlussunna. Kuma sahabbai da dama sun yi bayani cewa matansa ba sa ciki, kamar Zaidu dan Arkam, kuma manzon rahama (s.a.w) ya nuna su da kansa.

Kai ya ishe mu cewa manzon (s.a.w) a farkon kiransa ya kafa wazirinsa kuma halifansa mataimakinsa a bayansa wato; Imam Ali (a.s) yayin da aka ce ya fara kiran danginsa “wanzur ashiratakal akrabinâ€‌ kuma littattafan ruwayoyi da tarihi da tafsirai duk sun yi nuni da hakan. Don haka wannan wani abu ne mai yanke hujja a fili, wannan yana nuna tafarkin jama’a mai tsira.

Ku nuna mini wata mazhaba da mai bin ta ko mai kafa ta tun asali ya yi da’awar cewa wannan ita ce tafarkin da shi kadai ne za a iya bi. Amma Imam Ali (a.s) ya bugi kirji ya yi da’awar cewa su ne Alayen Annabi wadanda wanda ya wuce su ya halaka haka nan wanda ya tsaya baya ya ki bin su ya tabe. Haka nan ma sauran imamai sha daya bayansa daga zuriyar Manzo (s.a.w) duk sun yi wannan kiran.

Manzon Allah (s.a.w) ya siffanta su da kasancewarsu su ne jirgin ruwan da wanda ya shiga ya tsira (wato kamar jirgin Annabi Nuhu (a.s)), kuma su ne aminci ga mutanen duniya, kuma kofar yafiya da sauran kalmomi da suke nuna cewa duk wanda bai bi su ba, to ya tabe.

Kuma dukkaninsu ba su da sabawa tsakaninsu, kowannensu yana karfafa abin da magabacinsa ya fada ne, ka duba maganganun wadannan tsarkaka sha hudu, wato; manzon rahama (s.a.w) da alayensa sha biyu (a.s) kuma wasiyyansa kuma halifofinsa, ka kuma duba maganar â€کyarsa Zahara (a.s) ka duba mini in ka taba ganin inda wani ya fada wani ya warware koda kuwa waje daya don Allah ka gaya mini.

Wasiyya da su hatta da wadanda suke toshe falalolinsu a wurare da dama amma sun kasa boye komai game da su, Duba ka gani mana a tafsirin ayar nan ta “Kawai majibancin lamarinku (Jagoranku) Shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadanda suke tsayar da Salla suke bayar da Zakka alhalin suna masu ruku’uâ€‌. sai ga shi ya zo a littafin tafsirn Ibn Kasir: a tafsirin wannan aya ta 55 ta Surar Ma’ida cewa: Daga Maimun dan Mahran daga Ibn Abbas, a fadin Allah mai girma da buwaya. “Kawai majibancin lamarinku (Jagoranku) Shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadanda suke tsayar da Salla suke bayar da Zakka alhalin suna masu ruku’uâ€‌. Yana mai cewa: Ta sauka ne game da Muminai kuma Ali dan Abu Talib (a.s) Shi ne na farkonsu. Wato tana mai nuni da cewa na farkon wadanda za a mika wa wilaya da Shugabanci bayan Allah da Manzonsa shi ne Ali (a.s) Sa’annan masu biyo wa bayansa na daga wasiyyai, kamar yadda hadisi yake cewa; Ali ne na farkonsu. Kuma kamar yadda zamu ga ayar ta sauka ne a lokacin da ya yi sadakar zobensa alhalin yana cikin ruku’i. Wasu littattafan suna cewa; ta sauka game da muminai Ali (a.s) ne na farkonsu, Mahadi (a.s) na karshensu. Sai suka kawo cewa Imam Mahadi (a.s) ne na karshensu. Ina ganin wannan kadan ke nan daga abin da zan kawo maka.

Amma bayan sunnarsu babu wata Sunna ta wani mutum daga mahaluki koda kuwa waye da Allah da manzonsa suka ce a bi, bayan sunnarsa da sunnar wadannan halifofi nasa, don haka aikinsu da zancensu da tabbatarwarsu ta zama hujja saboda Allah da manzonsa ne suka gaya mana haka cewa a yi riko da su kuma su tsarkaka ne, domin sun san sunnarsu ba zata taba sabawa sakonsu ba.

Amma a sauran mazhabobi babu wanda ya bigi kirji ya ce mazhabarsa ba ta cike da kuskure, ko yana da hujja daga Allah (S.W.T) da Manzo (a.s)  cewa a bi shi.



1 2 next