Dahariyya



Dahariyya

Wannan Hadisi ruwaya ce daga Sadiku Ahlil Bait (A.S) game da tattaunawar Manzo da Ma'abota wannan addini wanda a cikinsa akwai usulubi mai kyau na muhawara da ma'abocin wata Akida da ta saba ta da mai muhawara, wanda a cikinta zamu koyi muhawara da mukabala da munazara da hanyar da take mafi kyau kamar yadda aka yi umarni da (Bil lati Hiya Ahsan). Yana kuma koyar da Hanyoyin kafa dalili Mubashir wato dalili na kai tsaye da kuma Gaira mubashir, da kuma Jawabil halli wato Hanyar warwara da kuma Jawabin Nakdi, wato Hanyar kama mutum da abin da ya yarda ya kuma yi imani da shi. A lokaci guda kuma yana iya nuna mana hakikanin manufar wannan Addini da yadda ma’abotansa suke fassara Akidojinsa. Kuma tana nuna mana yadda aka canja koyarwar Addinin da ya gabata, al'amarin da wannan al'umma ba ta tsira daga irinsa ba ta hanyar riko da Raunanan maganganu ko kuma Tafsirin da ya kafu bisa mahanga ta kuskure da yakan kai ga kurakarai wajan fahimtar Addinin Allah.

Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su, al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ma ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su zuwa ga rarraba zuwa Mazhabobi da Kungiyoyi na Akida daban daban. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu, domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya a kuma kautar da Akidunsu daga sahihancinta kamar Yahudawa da Kiristoci da Zartush da Sa’ibawa da sauransu. Amma wannan al’umma Allah ya yi alkawarin kare littafinta, shi ya sa ma duk wanda yake ganin wani yana da Alkur’ani daban da wanda yake hannun musulmi to yana ganin Allah Ajizi ne daga alkwarin da ya dauka na kare littafinsa, kuma irin wadannan mutane suna a matsayin wadanda suka kafirce wa Allah ta hanyar kafircewa Ayar Alkur’ani mai girma.

MUNAZARAR MANZO (S.A.W)

Imam Assadik (A.S) ya ce: "Daga Babana Albakir (A.S) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (A.S) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (A.S) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (A.S) cewa, wata rana ma’abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (S.A.W); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.

Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (A.S) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (A.S) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai . Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan ala’amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce Allah (S.W.T) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

DAHRIYYA

Sa’annan sai ya fuskanci ‘yan Dahriyya ya ce da su: Me ya sa kuke cewa abubuwa ba su da farko ba su da karshe?. Kuma ba su gushe ba kuma ba sa gushewa?. Sai suka ce: Domin mu ba ma hukunci sai da abinda muka gani, ba mu kuma samu farko ga abubuwa ba sai muka yi hukunci da cewa ba ta gushe ba tun farko samammiya ce, ba mu gan ta tana karewa ba sai muka yi mata hukunci da cewa ita Mai dauwama ce. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin kun same ta Maras farko ko kun same ta Mai wanzuwa har abada ba za ta gushe ba?. Idan kuka ce: Kun same ta hakan, to kun tabbatar wa kawukanku cewa ba ku gushe ba a kamanninku da hankulanku ba ku da farko kamar yadda ba zaku gushe ba a halinku kamar yadda kuke, idan kuma kuka ce haka, to kun yi musun hakikanin zahiri kuma masana wadanda suke ganinku zasu karyata ku.

Sai suka ce: A’a, mu ba mu ga farko gare ta ba kuma ba mu ga karshe gareta ba. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Saboda me kuke hukunci da rashin farkonta da rashin karshenta har abada ga ku ba ku ga farkonta ba, kuma karewarta shi ya fi cancanta ya wakana fiye daga bayanin da irinku yake yi game da ita, sai a yi mata hukunci da faruwa da karewa da yankewa domin ba ku ga dadewa ko wanzuwa gareta ba har abada.

Ba kuna ganin dare da rana ba?. Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin kuna ganinsu ba su gushe ba kuma ba zasu gushe ba? Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin yanzu ya halatta ku yi hukunci da haduwar dare da rana waje daya?. Suka ce: A’a. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ashe kenan kowannensu rabe yake da dayan sai daya ya riga daya ya zama duk inda daya ya yanke dayan yana gudana bayansa. Suka ce: Haka yake. Sai ya ce: Kun yi hukunci a nan da faruwar abinda ya gabata na daga dare da rana alhalin kuma ba ku gan su ba, saboda haka kada ku musa wa Allah ikonsa.

Sa’annan sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin kuna cewa duk abinda ya gabata na daga dare da rana yana da karshe ko ba shi da karshe? Idan kun ce: Yana da karshe, to kun sami karshen da ba shi da farkonsa, idan kuma kuka ce: Yana da karshe to an sami lokacin da babu wani abu da ya kasance daga cikinsu. Sai suka ce: Na’am.

Sai ya ce da su: Shin kun ce Duniya Dadaddiya ce ba Fararriya ba kuna sane da ma’anar da kuke nufi da furucin da kuka yi da kuma abin da kuke musawa? Suka ce: E. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Wannan halittu da kuke gani sashensu suna bukatuwa zuwa ga sashe, domin kowanne ya dogara ne ga samuwa da daya sashen nasa kamar yadda zaku ga gini sashe yana bukatar sashe, in ba haka ba, da bai yi karfi ba bai hadu ba haka ma sauran abubuwan da muke gani.



1