Bada'i(Canjawa)Sai dai idan muka zurfafa tunani kan ma’anar Bada a ma’anarsa ta lugga to zamu same shi yana hauhawa daga abu biyu ne: 1-Jahilci da ya rigaya. 2-Canjin ra’ayi da manufa da hadafi sakamakon sabon ilimin da aka samu. Sai mu tambaya wanne ne daga wadannan al’amura guda biyu yake kore Tauhidi? Na farko ko na biyu? Kuma shin zai yiwu a raba tsakaninsu? Ta yadda za a samu wani canji a ra’ayi ba tare da ya kasance daga jahilci da ya rigaya ba ko kuma ilimi sabo da ya faru ba? Amma tambayar farko: Zamu ga cewa a sarari yake cewa al’amari na farko yana kore tauhidi, kuma babu wani musulmi da ya karbi jingina wa Allah madaukakin sarki jahilici. Amma abu na biyu: Idan canji ya zama yana lizimtar zati domin jahilci da ya gabata ne da kuma samuwar ilimi da ya zo. to a nan yana kore tauhidi, kamar yadda jahilci yake kore tauhidi haka ma canji yake kore shi. Amma idan canji ba ya samun zati yana faruwa daga wani abu daban to anan ba ya kore Tauhidi. Wanna canjin na ra’ayi da yake lizimtar zati domin bayyanar ilimi da kuma bacewar jahilci, saboda haka ne kamar yadda ba zai yiwu a jingina jahilci ga Allah ba haka nan ba zai yiwu a jingina masa canji a ra’ayi ba (S.W.T) domin wannan yana nuna ilimi ne da aka samu, alhalin ilimin Allah ba wanda ake nema ba ne domin a samu. Shi iliminsa na zatinsa ne wanda yake shi mai tsayuwa ne da samuwar zatinsa. Da wannan ne jawabin wadanna tambayoyi biyu ya bayyan a fili, kuma bari mu gani shin akwai aya a kur’ani da ta dangantawa Allah canji a wani al’amari, ko wani bangare? Akwai wadanda sukan amsa cikin gaggawa game da wannan suna masu cewa alkur’ani mai girma ya kore duk wani canji ga Allah (S.W.T) suna masu dabbaka wannan aya: “Ba zaka taba samun juyi ba ga sunnar Allahâ€[3]. “Ba zaka taba samun canji ba ga sunnar Allahâ€[4].
|