Ajali KoWa'adi



[11] Gurarul hikam: 4239.

[12] Albihar: 5/140/7.

[13] Al’an’am: 2.

[14] Albihar: 5/139/3.

Fifita Wasu

Fifita wasu a kanmu yana daga cikin manyan dabi'u da aka yi umarni da koyi da su a addinin musulunci madaukaki, da wannan halin mai girma ne aka samu cigaba a wannan duniya kuma aka samu daidaita lahira, idan babu wanan hali to fa ba yadda za a yi a samu sadaukarwa da kokarin kai domin samar da gyara da horo da kyakkyawa da hani daga mummuna a cikin al'umma, wasu ruwayoyi sun zo da cewa ita wannan dabi'a ta fifita wasu a kan kawukanmu tana daga mafifitan halaye na gari[1], kuma alama ce ta bayin Allah na gari[2].

Yawancin abin da ya sanya al'ummarmu ci baya a wannan zamanin ya taso ne daga rashin wannan halayya mai kyau ta gari, kuma abin da ya sanya al'ummar farko da ta tare a gefen Manzon Allah (s.a.w) shi ne ta kasance mai fifita wasu a kanta don haka ne ma aka samu cigaba. Kuma Allah madaukaki ya yi yabo game da wannan hali da mutanen da suka siffantu da shi a fadinsa cewa: "Suna fifita wasu a kan kawukansu koda kuwa su suna da bukata"[3].

Sannan kuma muna ganin wasu ruwayoyin sun siffanta wannan dabi'a mai kima da daraja da cewa ita ce mafi kyawun kyautatawa, kuma mafi darajar matakan imani[4]. Ko kuma ita ce mafificiyar ibada, kuma mafi girma a jagoranci[5].

Wannan lamarin ba komai yake nuna mana ba sai cewa; wannan siffa tana kunnen doki da salla, domin an siffanta ta da mafificiyar ibada kamar yadda ruwayoyi game da salla suka zo suna fifita ta da wadannan siffofin masu kima da daraja, na biyu suna nuni zuwa ga cewa babu siffa mafi girma ga shugaban al'umma kuma jagoransu da ta kai wannan siffar girma, kuma dukkan jagora dole ne ya siffantu da ita.

A nahiyoyi irin namu babu wani abu da ya kawo mana ci baya fiye da nisantar wannan siffa madaukaki da kusantar siffofin da suke kishiyantar ta wadanda suke munana kamar son kai, da fifita kawukanmu a kan wasunmu. Idan mun duba sosai zamu ga jagororin al'umma suna sace dukiyar al'umma kuma suna nuna halin ko in-kula da ita, sannan kuma suna da karancin nuna abin da ya damu wannan al'ummu nasu na musibu da bala'o'i, kuma sun kebanci kansu da kula ta musamman kamar zuwa kasashen ketare don magani da kula da lafiyarsu da kuma mafi girman bala'in da ya kawo mana jahilci ya yi yawa sakamakon sun kebanci kansu da su da dukkan masu karfi da dukiya da makarantu, sai makarantun 'ya'yan talakawa suka rage babu wani abin azo-agani da suke da shi, ga karancin kulawa da abin da suke ciki, to fa wannan duka ya taso ne daga mummunar siffar nan ta nisantar fifita juna da son kai, da fifita kawukansu a kan wasunsu.

Imam Ali (a.s) ya kasance ba ya bacci sai ta tabbatar da babu wani mutum da yake cikin yunwa, kuma yana fifita wasu a kansa da komai tun daga wurin zama har a abin sawa da kuma rabon arzikin kasa, don haka ne ma sai hukumarsa ta kasance abin buga misali a adalci a duniya kuma gun dukkan ma'abota addinai daban-daban har ranar da kiyama zata tashi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next