KebantattunAl’amuran Mahangar Shi'aWasu daga ayyukan da suka faru a lokacin wannan boyuwar tasa babba mai tsayi sun hada da: 1- Tseratar da musulmi daga hannun karkatattun sarakuna masu kauce wa hanya. 2- Tseratar da wasu jama’ar musulmi daga hannun wasu ‘yan fashi da masu tare hanyar matafiya da karauka. 3- Gargadin ga mutane da tsoratar da su, da nuna musu cewa har yanzu sharuddan bayyanarsa ba su cika ba, kuma mutane ba a shirye suke da su dauki wannan nauyi mai girma ba. 4- Mayar da Hajarul aswad wajan da yake a Ka’aba a shekarar 339 ko 337 bayan harin Karamida zuwa Makka a sherkarar 317 da suka dauke dutsen Hajarul aswad. 5- Bayar da labarin wasu abubuwa muhimmai na siyasa da al’umma kafin mutane su sani. 6- Nasiha da son alheri ga mutane da kuma kama hannunsu da dora su kan tafarkin kyawawan halaye. 7- Bayar da taimakon dukiya ga wasu. 8- Warkar da masu cututtuka masu nakasa wadanda likitoci suka kasa yin maganinsu. 9- Nuna wa wadanda suka bace a Sahara hanya da kuma isar da wadanda aka bari a baya zuwa ga ragowar karauka. 10- Koyar da addu’a da zikiri masu madaukakan ma’anoni ga wasu mutane. 11- Dagewar imam Mahadi (A.S) a kan karanta addu’o’in kakanninsa tsarkaka wadanda suke kunshe da ma’anoni madaukaka, da hakikanin gaskiya da imani, wadanda an rubuta misalansu da yawa[19]. [1] Ma’ida: 3.
|
back | 1 2 3 4 5 6 |